Zamfara: Matawalle zai kashe N7bn don gina sabuwar gidan gwamnati

Zamfara: Matawalle zai kashe N7bn don gina sabuwar gidan gwamnati

- Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 7 a kasafin kudin jihar don gina sabon gidan gwamnati

- Kamar yadda sakataren gidan gwamnatin jihar ya bayyana wa majalisar jihar, tun dama gidan gwamnatin jihar na wucin-gadi ne

- Gina sabon gidan gwamnati a jihar zai shawo kan matsalolin rashin ofisoshi da ke addabar jihar kuma za a mayar da tsohon gidan gwamnatin zuwa sakateriya

Gwamnatin jihar Zamfara ta ware naira biliyan 7 a kasafin kudinta na shekarar 2020 don gina sabon gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar, Bala Bello ya sanar.

Bello ya bayyana hakan ne a Gusau a ranar Alhamis, a yayin kare kasafin kudin ofishinsa a gaban majalisar jihar.

Bello ya ce gwamnatin jihar ta yanke hukuncin gina sabon gidan gwamnati ganin yadda jihar ke matukar bukatar hakan.

DUBA WANNAN: 2023: Ɗankwambo ya aike wa 'yan PDP saƙo

"Kun san cewa gidan gwamnatin jihar shine tsohuwar sakateriyar karamar hukumar Gusau a tsohuwar jihar Sokoto, anyi amfani dashi ne a matsayin gidan gwamnati na wucin-gadi a lokacin da aka kirkiri jihar a 1996." ya ce.

"Muna da bukatar sabon gidan gwamnati na zamani don ya dace da zamanin da jiharmu ke ciki a wannan kasar. Muna kuma tunanin gina sabon gidan gwamnatin ne don mu shawo kan matsalar rashin wadatuwar ofisoshin dake damun gidan gwamnatin," ya kara da shi.

"Idan aka kammala wannan aikin, gidan gwamnatin yanzu za a mayar da ita sakateriya ne," in ji shi.

A halin yanzu, gwamnatin jihar ta ware naira miliyan 700 daga cikin kasafin kudin jihar don tallafa 'yan gudun hijirah tare da taimakawa wadanda wani iftila'i ya fada wa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel