Babbar diyar marigayi Abacha ta rabu da mijinta dan kasar Kamaru

Babbar diyar marigayi Abacha ta rabu da mijinta dan kasar Kamaru

Gumsu Abacha 'yar tsohon shugaban kasa Najeriya ce ta mulkin soji, Sani Abacha. Gumsu ta aura Bayero Fadil Mohammadou ne kusan shekaru 20 da suka gabata. Bayero ya kasance babban mashahurin mai arziki ne dan asalin kasar Kamaru.

Ma'auratan sun yi aure ne tun a shekarar 1999 amma sai zaman ya kare a 2019. Sun rabu ne sakamakon wasu banbance-banbance da ba zasu iya shawo kansu ba a cikin wannan shekarar.

Bayero, tsohon mijin Gumsu ya bayyana wannan labarin ne a cikin kwanaki kadan da suka gabata. Ya bayyana hakan ne a yanar gizo inda yace sun rabu ne sakamakon wasu banbance-banbance ne da ba zasu iya sasantawa ba.

Tsoffin ma'auratan sun haifa kyawawan 'ya'ya biyar kuma zasu cigaba da kula da 'ya'yan tare.

DUBA WANNAN: Badakalar daukan aiki: Matawalle ya dakatar da wasu manyan ma'aikatan gwamnatin Zamfara

A wani labari na daban, Legit.ng ta ruwaito cewa, sanannen basaraken kasar yarbawa, Oluwo na kasar Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi ya saki matarsa mai suna Chanel Chin. Hakan ya bayyana ne daga wallafar da ya yi a shafinsa na Instagram a ranar 15 ga watan Disamba, 2019.

A takardar da sakataren yada labarai na Sarkin yasa hannu, basaraken ya bukaci jama’a, abokai da makusanta da su kiyaye duk wani kasuwanci ko bukata da aka yi amfani da ofishin sarauniyar.

Kamar yadda Ibraheem ya sanar, auren ya rabu ne saboda ‘dalilian da ba za a iya sasantawa ba’. “Ana sanar da jama’a ballantana abokai da makusantan Oluwo na kasar Iwo, a kan cewa mai martaba Oba (Dr.) Abdulrosheed Adewale Akanbi, Telu I, cewa Chanel Chin a halin yanzu ta zama tsohuwar sarauniyar mai martaba.

“Wannan labarin ya zama wajibi don gudun bada wani girma da yake da dangantaka da karagar mulkin Oluwo din gareta. A saboda dalilin banbanci wanda ba zai sasantu ba, Chanel Chin ta rabu da Sarkin kuma a halin yanzu ba sarauniyarsa bace."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel