Ban taba ganin shugaba mai bin tsarin demokradiyya kamar Buhari ba - Yahaya Bello

Ban taba ganin shugaba mai bin tsarin demokradiyya kamar Buhari ba - Yahaya Bello

- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya ce shugaba Muhammadu Buhari ne shugaban kasa mafi biyaya ga ka'idojin demokradiyya da ya taba sani a rayuwarsa

- Gwamna Bello ya ce shugaban kasar ya nuna cewa tsohon Janar na mulkin soja zai iya sauya wa ya rungumi demokradiyya har ya rika barin wasu abubuwa na faruwa

- Gwamnan ya kuma yi Allah wadai da sukan da wasu ke yi kan salon mulkin na shugaba Buhari a kasar

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya yi Allah wadai da sukar da wasu ke yi kan salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwaman ya ce bai taba ganin wani shugaban kasa a Najeriya da ke kauna da biyaya ga tsarin demokradiyya ba kamar Shugaba Muhammadu Buhari.

A hirar da ya yi da Daily Trust, gwamnan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nuna cewa tsohon Janar na Soja kan iya sauya wa ya rungumi demokradiyya har ya rika barin wasu abubuwa na faruwa.

DUBA WANNAN: Yadda wata amarya ta daure fuska a hoton auren ta ya dauki hankalin mutane

Ya ce, "Shugaban kasa ne shugaba mafi biyaya ga tsarin demokradiyya da na taba gani. Wannan shine karo na farko da muke ganin tsohon shugaban mulkin soja ya rungumi tsarin demokradiyya har ta kai ga ana aikata wasu abubuwa kuma yana kawar da kai baya magana a kansu."

"Duk wanda ke kiransa mai mulkin kama karya, ina tunanin wannan mutumin shine mai mulkin kama karyan ba Shugaban kasa ba," a cewar Gwamna Bello.

Da ya ke magana a kan harkokin jihar Kogi, gwamnan ya ce yana ta kokarin sasanta tsakanin al'umma domin tabbatar da hadin kai bayan zaben gwamna da aka gudanar a jihar a baya-bayan nan.

Ya ce gwamnatinsa ta dau alwashin tafiya tare da dukkan al'ummar jihar don tabbatar da cigaban jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel