Ganduje zai kashe naira biliyan 2.5 don gina manyan asibitoci a sabbin masarautu

Ganduje zai kashe naira biliyan 2.5 don gina manyan asibitoci a sabbin masarautu

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje ya amince da kashe naira 2,543,819.67 don gyaran wasu asibitoci a sabbin masarautun jahar Kano guda hudu na Gaya, Rano, Karaye da Bichi tare da fadada su.

Kwamishinan watsa labaru, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru bayan kammala taron majalisar zartarwar jahar karo na uku daya gudana a fadar gwamnatin jahar Kano.

KU KARANTA: Musulmai ba za su amince da dokar daidaita maza da mata a rabon gado ba - Sultan

Jaridar Solacebase ta ruwaito kwamishinan yace daga cikin ayyukan da za’a aiwagar a cibiyoyin kiwon lafiyar akwai ginin bangaren kula da hatsari da aikin gaggawa, dakin marasa lafiya mai cin gado 22, bangaren ido, bangaren kunne, makogwaro da hanci, bangaren hakori, sashin kula da kashi da dakin gwaje gwaje.

Sauran kuma sun hada da bangaren ajiyan gawarwaki, ginin sabbin hanyoyi, kawata asibitin da furanni, samar da ruwa da tankunan ajiyan ruwa da dai sauran ababen da zasu saukaka gudanar da asibitocin.

Bugu da kari kwamishinan yace gwamnati za ta gudanar da gyare gyare a bangaren kula da yara, ofisoshi, dakunan ajiyan kayayyaki, dakunan bayar da magunguna, sashin karbar haihuwa, sashin tiyata, dakin daukan hoto da sauran bangarorin asibitocin dake masarautun hudu.

Haka zalika gwamnatin Ganduje ta amince da sayo kayan aikin tare da zubasu a sabuwar asibitin kula da cutar daji watau Cancer da jahar za ta gina, a kan kudi naira biliyan 4.2, manufar hakan shi ne inganta kiwon lafiya a jahar, inji shi.

A cigaba da jawabinsa, kwamishina Garba ya bayyana cewa gwamnatin ta amince da kafa sabuwar makarantar mata ta kwana ta kimiyya da fasaha a garin Ganduje, cikin karamar hukumar Dawakin Tofa a kan kudi naira miliyan 165.

A wani labari kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana rashin amincewar al’ummar Musulmai da kudurin dokar daidaita maza da mata a kan abin da ya danganci rabon gado.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Sultan ya bayyana kudurin dokar a matsayin abin da ya saba ma dokokin addinin Musulunci, don haka Musulman Najeriya ba zasu taba amincewa da ita ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel