APC: Manyan 'yan siyasa 5 da zasu iya taimakon Tinubu ya cimma burinsa a 2023

APC: Manyan 'yan siyasa 5 da zasu iya taimakon Tinubu ya cimma burinsa a 2023

Babban jigon jam’iyyar APC ya yi matukar kokari wajen tabbatar da yuwuwar mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Tun daga hawan shi mulki na farko har zuwa tazarcensa a 2019. Hakan yasa mutane suke tunanin ko zuciyarsa ta darsu da son wannan kujerar ta kololuwar mulkin Najeriya.

Zata iya yuwuwa kuma akwai wani yarjejeniya dake tsakanin Jagaban masarautar Bolu din da shugaban kasa Muhammadu Buhari duk da kuwa shirin wasu ‘yan Arewa.

Ga mutanen da zasu iya taka rawar gani wajen tabbatar da yuwuwar cikar burin wannan gogaggen dan siyasar na samun mulkin kasar Najeriya.

1. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

Goggagen dan siyasa Bola Tinubu ne ya zabo Farfesa Yemi Osinbajo don ya zamo mataimakin Shugaba Buhari a yayin zaben 2015. Wannan kuwa yayi sanadin ture mulkin PDP.

2. Gwamna Fashola

A halin yanzu minister ne a gwamnati. Ba minister kadai ba, mutum ne da Buhari ke matukar ganin girmansa.

DUBA WANNAN: A yayin da ake rade- radin mutuwarsa, IBB ya bayyana shirinsa na yin aure bayan shekara 10 a matsayin gwauro

3. Gwamna Rauf Aregbesola

Wannan babban dan siyasa ne kuma mai fadi a ji a siyasar kudu maso yamma a Najeriya. Tsohon gwamnan jihar Osun ne kuma yaron Tinubu ne.

4. Gwamna Sanwo Olu

Shi ke shugabantar jihar Legas a halin yanzu. Idan zamu tuna, Tinubu ne ya jawo hannunsa tare da dora shi a matsayin dan takarar gwamnan APC har aka zabesa a matsayin gwamnan jihar Legas. Akwai yuwuwar ya biya Tinubu wannan karamcin.

5. Gwamna Nasir El-Rufai

Wannan zai iya zama abun mamaki a gareku, amma siyasa ce kuma tamkar caca ce. Ba shakka Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ba zai ki tayin mataimakin shugaban kasa ba idan aka yi masa. Hakazalika zai iya taka rawar gani don samun wannan nasarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel