Kano: An bayyana hukuncin da za a zartarwa mai adaidaita sahu da aka kama ya dauki namiji da mace

Kano: An bayyana hukuncin da za a zartarwa mai adaidaita sahu da aka kama ya dauki namiji da mace

Hukumar Hisbah ta Kano a ranar Alhamis ta ce duk wani mai adaidaita sahu da aka kama yana daukan mata da maza a lokaci guda zai fuskanci hukuncin bulala 10 ko a dakatar da shi daga aiki na tsawon watanni shida.

Shugaban Hisbah, Harun Ibn-Sina ya shaidawa Premium Times cewa za a bawa wadanda aka samu da laifin zabin biyan tarar N5,000 idan kuma ba haka za su fuskanci hukunci daidai da irin laifin da suka aikata.

A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda gwamnatin na jihar Kano da sake dawo da dokar ta hana gwamutsa mata da maza a cikin keke napep guda a yunkurin ta na dabbaka koyarwar addinin musulunci na kare mutunci da kimar mata a jihar.

Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Janairun 2020.

DUBA WANNAN: Giwaye 250 aka hango a filin dagar Boko Haram

Kwamandan na Hisabah ya ce duk wani direban adaidaita sahu da aka kama yana dauke da mata da maza a lokaci guda ya aikata laifi a karkashin dokar tuki na jihar Kano da aka yi wa kwaskwarima a 2005.

Da zarar an kama direban, za a garzaya da shi kotun tafi da gidan ka, kotun majistare ko kuma kotun Shari'ah.

Ibn Sina ya ce dokar ba ta shafi ma'aurata ba, da kananan yara da kuma 'yan gida daya. Ya ce an dauki matakai da suka dace domin ganin samun nasarar aiwatar da dokar tare da goyon bayan hukumar kiyaye cinkoson ababen hawa ta Kano (KAROTA) da sauran hukumomi.

Wani lauya mazaunin Kano, Rabiu Rijiyar Lemu ya ce dokar da Hukumar ta Hisbah ta fitar zai kawo matsala tsakanin masu adaidaita sahu, fasinjoji da jami'an tsaro a jihar.

Rijiyar Lemu ya ce, "Idan Hisbah ba za ta iya gabatar da rubutaccen doka da ke bayani kan bulala ko dakatarwar na watanni shida ba tare da cin tarar N5,000 kan gwamutsa maza da mata, dokar ba za tayi aiki ba don ta ci karo da sashi na 36 na kudin tsarin mulkin kasa ta 1999."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel