Sai hakuri abin a jinina ne, bazan iya dainawa ba - In ji matar da aka kama ta kwanta da maza 100

Sai hakuri abin a jinina ne, bazan iya dainawa ba - In ji matar da aka kama ta kwanta da maza 100

- Akwai yiwuwar mu ci amanar abokan zamanmu idan muka gano hakan halayyar iyayenmu ce

- A sabon binciken da aka gudanar a kwanan nan, an gano cewa wadanda suka ga ana halayyar cin amana a gidansu sun fi yi

- Wata mata ta bayyana yadda ta kwanta da maza sama da 100 na aure kuma ta jaddada cewa a cikin jininta yake

Akwai yiwuwar mu ci amanar abokan zamanmu idan har hakan halayyar iyayenmu ce? Kamar yadda sakamakon wani bincike ya nuna, akwai yiwuwar mata biyu bisa uku da iyayensu mata suka taba cin amana, su ma su ci amanar abokan rayuwarsu.

Kusan kashi daya bisa uku na matan da aka gudanar da binciken a kansu sun ce, suna tunanin halayyar cin amanar iyayensu mata ce ta sa suke cin amanar abokan rayuwarsu. Hakan kuma yasa wannan halayyar cin amanar take bibiyar danginsu.

Hakazalika, an gano cewa maza na cin amanar abokan rayuwarsu ne sau da yawa in suka gano cewa iyayensu maza na wannan halayyar. Sama da kashi 52 na mazan da ke cin amanar matansu, sun bayyana cewa sun ga iyayensu maza na yi ne.

Wannan binciken yasa ma’abota binciken, yanke hukuncin cewa akwai yuwuwar cewa ana iya gadon cin amanar abokan rayuwa. Wata mata kuwa ta tabbatar wa da masu binciken gaskiyar lamarin.

KU KARANTA: Bincike: Cin zogale ga mata masu ciki na da matukar illa ga jariran cikinsu

Matar mai suna Gweneth Lee, ta bayyana cewa tayi mu’amala da maza sama da 100 kuma masu aure a cikin shekaru 10 kacal. Matar mai shekaru 47 daga Chelsea a birnin Landan ta bayyana cewa: “Cin amana yana bin tsatso. ‘Ya’yan masu cin amana basu tunanin fushin iyayensu in suna kamanta irin halayyarsu. Daya daga cikin mazan da na taba mu’amala dasu, babban ma’aikacin banki ne daga Cambridge. Mahaifiyarshi ta yi aure har sau uku.

“Ya girma tare da ita ne ya kuma lura da cewa tana mu’amala da maza kala-kala. Mahaifiyarshi ta san yana bin matan banza amma sun barshi a sirri don gudun matarshi ta sani.”

Gweneth ta fara neman mazan aure ne don lalata bayan da mijinta mai suna Robert ya mutu. Ta bayyana cewa, wasu daga cikin kawayenta mata masu aure suna bibiyar mazan waje. Wannan ke nuna cewa, ita cin amana a cikin jininta yake kuma daga tsatsonta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel