Bakin kishi yasa na kashe'yar gidan kishiyata - Aisha Abubakar

Bakin kishi yasa na kashe'yar gidan kishiyata - Aisha Abubakar

- A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta gabatar da wata mata da ta kashe 'yar kishiyarta

- Mahaifiyar yarinyar mai shekaru hudu a duniya, itace amarya a gidan Malam Abu

- Aisha Abubakar ta bayyana yadda ta zuba wa yarinyar guba a cikin abincinta inda ta ci ta garzaya lahira

A satin da ya gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta gabatar da wata mata mai suna Aisha Abubakar da ke sabuwar unguwa a karamar hukumar Rimi a jihar. Ana zarginta da kashe 'yar kishiyarta ta hanyar zuba mata guba a cikin abinci.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isa ne ya gabatar da wadda ake zargin ga manema labarai a madadin kwamishinan 'yan sandan jihar.

Ya bayyana cewa, yarinyar da aka kashe mai suna Aisha tana da shekaru uku ne kacal a duniya. Ita ce ta biyu a wajen mahaifiyarta mai suna Hadiza. Hadiza ce amarya daga cikin mata hudu da Malam Abu Fardami mai gyaran fanfo ke dasu. Ma'aikaci ne a karamar hukumar Rimi.

KU KARANTA: An yiwa wani mutumi bulala 12 akan ya saci biredi

Da take bayyana yadda abun ya faru ga 'yan sanda, Aisha ta ce marigayiyar na cin abinci ne tare da 'ya'yanta biyu. Ta haka tayi amfani da wannan damar don zuba guba a gabanta kuma ta hana 'ya'yanta cin abinci. Ta ce su bar wa Aisha ita kadai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel