Tirkashi: Ku raba ni da ita, ta yi zina da maza har tara - Miji mai neman saki

Tirkashi: Ku raba ni da ita, ta yi zina da maza har tara - Miji mai neman saki

Wani ma'aikacin gwamnati mai suna Sunday Udo, a ranar Alhamis ya roki wata kotun kwastamari da ke Abuja da ta warware aurensu mai shekaru 28. Ya yi ikirarin cewa, matarsa ta kwanta da maza 9 duk da aurensa da ke kanta.

Udo ya bayyana zargin nan ne a yayin da ya mika kokensa gaban kotun na tsinke igiyar aurensu.

"A lokacin da muka yi aure, muna zama ne a Legas. Bayan haihuwarmu ta fari, ta je gida don ganin iyayenmu. A maimakon taje wajen iyayena, sai ta zarce wajen iyayenta,"

"A lokacin ne ta fara mu'amala da maza daban-daban wanda da bakinta ta sanar min. Tace ta kwanta da maza tara," in ji shi.

Udo ya sanar da kotun cewa ya kai kararta wajen sirikinsa wanda ya kushe wannan mummunan halayyar.

DUBA WANNAN: Kano: Bidiyon yadda masu neman aiki ke haura katanga da taga a hukumar NDLEA ya janyo cece-kuce

"Na kai kararta wajen mahaifinta. Mahaifinta ya tambayeta ko ta fara hauka ne, don munin abinda tayi. Na sanar da mahaifiyarta ma, amma sai ta shawarceni da in dauki matata da da na mu koma birni," inji mai kara.

Udo ya sanar da kotun cewa, matarsa na tafiya kamfen din siyasa ba tare da izininsa ba.

"Mata ta ta shirya tafiya da daya daga cikin samarinta kuma har suka yi sati uku a tare," in ji shi.

Udo ya roki kotun da ta tsinke igiyar aurensu kawai ya huta.

Alice Udo itace matar da ake zargi, ta sanar da cewa a shirye take don kare kanta kuma lauyanta zai hallara a zaman kotu na gaba.

Alkali Jemilu Jega, ya shawarci mai karar da ya sasanta da matarsa. Ya ce: "A halin yanzu kai kaka ne, duk budurwar da tace maka tana sonka ba zai wuce aljihunka take hange ba," a cewar Jega.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel