Budurwa tayi kokarin kashe kanta domin ta dorawa saurayinta laifi saboda ya rabu da ita

Budurwa tayi kokarin kashe kanta domin ta dorawa saurayinta laifi saboda ya rabu da ita

- Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumunta ta tuwita ta firgita mutane da tsokacin da ta yi

- An tambaya ne a kan wanne rashin hankali ko hauka mutum zai iya bayan ya rabu da masoyinshi

- Budurwar ta bayyana cewa zata kashe kanta ne kawai ta yadda za a danganta mutuwar ga saurayin

Wata ma'abociya amfani da kafar sada zumuntar zamani ta tuwita ta bayyana abinda zata yi bayan ta rabu da saurayinta.

Ta sanar da hakan ne bayan da aka yi wata tambaya a kafar. An tambayi me mutum zai yi na hauka bayan rabuwa da masoyinshi.

Budurwar ta bayyana cewa zata kashe kanta ne, amma sai ta bada alamar da zata danganta kisan da saurayin. Ta yadda ta mutu amma ta sakashi a tsaka mai wuya.

Budurwar ta yi bayanin cin amanar da saurayinta ya yi mata tare da kawarta. Ta ce abun akwai bakin cikin tare da kunar rai.

"Zan kashe kaina ne kawai ta yadda za a danganta kisan dashi. Shine saurayina na farko kuma ya bata min rai ba kadan ba. Ya ci amanata ne da kawata." Cewar budurwar.

KU KARANTA: Tirkashi: An samu dan kamfe na 'yan mata sama da guda 100 a dakin wani saurayi

Wannan tsokacin kuwa ya tada hankula tare da ba ma'abota amfani da kafar sada zumunta mamaki ba kadan.

Ita tsananin soyayya, a wasu lokutan takan juye ta koma kiyayya. Duk kuwa mutumin da zai iya dangantaka da kisan kai, ba shakka ya zama makiyinka. Ko kotu bata yanke maka hukuncin kisa ba, ba shakka za a mutum shekaru masu yawa a gidan yari. Idan akwai rabon samu 'yanci ne Ubangiji zai wanke mutum ta wata hanyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel