Yadda wani tsohon dan gidan mari ya tsiyayewa wani mutum ido daya

Yadda wani tsohon dan gidan mari ya tsiyayewa wani mutum ido daya

Malam Salisu Yahaya mutum ne mai kimanin shekaru 40 a duniya, ya rasa idonsa ne a hannun wani dan daba mai suna Mario. Lamarin ya faru ne a unguwar Kwalwa da ke karamar hukumar birni da kewaye a ranar Litinin da ta gabata.

Mario ya daba wa Malam Salisu wuka a kwayar idonsa da wasu sassan fuskarsa.Hatsaniya ta sarke tsakanin Malam Salisu da Mario bayan da da daban ya mike kafa kan haya ya hana Malam Salisu wucewa.

Rahotanni sun nuna cewa, Mario na daga cikin wadanda aka sako daga gidan marin da gwamnatin jihar Kano ta rufe a kwanakin baya.

DUBA WANNAN: Yahaya Bello ya sadaukar da nasararsa ga mahaifiyarsa da al'ummar Kogi

Yayin zantawa da manema labarai, Malam Salisu ya ce, “Na dawo daga wajen mahaifiyata da na kai wa ziyara a unguwar Kwalwa sai na hadu da Mario a gefen titi. Na bukaci ya bani hanya in wuce amma sai ya ce bai san wannan ba. Bayan ‘yar hatsaniya da ta shiga tsakaninmu, kawai sai Mario ya fito da wata wuka daga aljihunsa. Ban yi aune ba naji ta a cikin kwayar idona da wasu sassan fuskata,”

Lokacin da lamarin ya faru, mutane da dama sun gani. Hakan ce ta sa suka kama Mario tare da mikasa ga hukumar ‘yan sandan Jakara. Amma daga bisani, an zargi DPO da sakin Mario.

A yayin da gidan rediyon Freedom ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, sai yace, "kamata yayi Yahaya ya shigar da karar DPO a kan tuhumar sakin Mario da ya yi. Daga nan ne ‘yan sanda zasu tsunduma binciken sahihancin labarin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel