Wuta ta kona gawarwakin mutane 12 a babban asibitin koyarwa

Wuta ta kona gawarwakin mutane 12 a babban asibitin koyarwa

Akalla gawarwakin mutane 12 suka kone kurmus a sakamakon wata gobara da ta tashi a sashin binciken ilimin halittar dan adam na babban asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife, jahar Osun.

Rahoton jaridar kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito wutar ta tashi ne da tsakar daren Talata, sai dai an yi sa’a jami’an hukumar kwana kwana dake cikin jami’ar tare da hadin gwiwar jami’an tsaron sun kashe wutar.

KU KARANTA: Yansanda sun tabbatar da kisan dan uwan Sanata Ibrahim Mantu

Kaakakin jami’ar, Abiodun Olarewaju ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, 19 ga watan Nuwamba, inda yace wutar ta fara ne da misalin karfe 3 na dare a sanadiyyar matsala da aka samu da wayoyin wuta.

Daga cikin gawarwaki guda 102 dake ajiye a dakin ajiyar gawar asibitin, gawarwaki 12 ne wutar ta shafa, kamar yadda daraktan watsa labaru na jami’ar, Abiodun Olarewaju ya tabbatar ma manema labaru.

“A yanzu haka sashin binciken ilimin halittar dan adam na asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo ta fara shirin sanar da iyalan mamatan da gawarwakinsu suka kone.” Inji shi.

Shi ma shugaban jami’ar OAU, Eyitope Ogunbode ya kai ziyarar gani da ido zuwa inda lamarin ya auku tare da sauran shuwagabannin jami’ar don ganin matsayin barnar da wutar ta yi, sa’annan ya bada umarni nan take domin a fara gyara.

Haka zalika shugaban jami’ar ya kafa kwamitin mutane uku domin su gudanar da cikakken bincike a kan musabbabin aukuwar gobarar. Zuwa yanzu dai hankula sun kwanta a jami’ar yayin da kowa ya kama harkar gabansa.

A wani labari kuma, rundunar Yansandan jahar Filato ta tabbatar da kisan wani dan uwan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, Hashimu Mantu.

Kaakakin Yansandan jahar, DSP Terna Tyopev ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, inda yace an gano gawar Hashimu ne a kauyen Chanso dake garin Gindiri, karamar hukumar Mangu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel