Ara: Wani karamin gari a Najeriya da babu kare ko guda

Ara: Wani karamin gari a Najeriya da babu kare ko guda

Mutane da dama suna amfani da karnuka wurin gadi, farauta ko kuma ajiye don sha'awa a gidajensu amma a garin Ara dake karamar hukumar Egbedore na jihar Osun an haramta kiwon karnuka. Tarihin karnuka a garin ne ya banbanta shi da sauran garurruwa.

Mutanen garin suna da karamci da tarbar baki sai dai dangantakarsu da kare abin tsoro ne. Duk karen da ya shiga garin ba zai fita da ransa ba kuma duk wani mazauni garin da aka kama yana kiwon kare zai fuskanci hukunci mai tsanani kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mafi yawancin mazauna garin ba su san ainihin dalilin da yasa aka haramtawa karnuka shiga garin ba. Galibinsu sun ce haka suka taso suka ji iyaye da kakanninsu na fadi hakan yasa suke raba jiha da karnuka ko da sun tafi zuwa wasu garurruwan.

Wani matashi mai suna Akin Ajao ya ce ya girma ne ya san cewa an haramtawa karnuka shiga Ara hakan yasa ya sha alwashin raba jiha da kare a rayuwarsa. Ya ce, "iyayen mu ba su taba yi mana gargadi game da kare ba, tarihi ne ya koyar da mu cewa an haramta alaka da kare a garin nan. A gaskiya ban san dalilin ba amma zan yi kokarin bincike."

Ara: Wani karamin gari a Najeriya da aka haramta kiwon karnuka

Ara: Wani karamin gari a Najeriya da aka haramta kiwon karnuka
Source: Twitter

Wata yarinya mai shekaru 12, Bolanle ta ce ba ta taba ganin kare ba kuma bata san yadda ya ke ba. Ta ce tana fatan za ta ga kare idan ta tafi wani garin ziyara duk da cewa itama ta san an haramta alaka da kare a garinsu.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan ta'adda da fuska a rufe sun kaiwa Gwamna Makinde hari a Kogi (Hotuna)

Ko a ranar cin kasuwar garin, mahauta da manoma daga garurruwan dake makwabtaka da Ara su kan ajiye karnukansu a bayan gari ne su shigo cin kasuwa domin ko baki da suka saba zuwa garin sun san cewa an haramta wa karnuka shiga garin.

Wasu masu rike da mukaman gargajiya da majiyar Legit.ng Hausa ta tattauna da su sun gaza fadin ainihin dalilin da yasa aka haramtawa 'yan garin hulda da karnuka inda suke ce sarkin garin ne kadai ke da ikon yin magana kan lamarin amma a halin yanzu babu sarki a garin tun bayan rasuwar sarki Oba Sunmonu Omolaoye a ranar 3 ga watan Fabrairun 2010.

Sai dai wani mazaunin garin na Ara, ma'aikacin gwamnati da ya nemi a boye sunansa ya yi magana kan lamarin. A cewarsa: "A wani lokaci mai tsawo da ya wuce, Sarkin Oyo ya bukaci sarkin Ara watp Alara ya kamo masa namun daji. Alara ya aika masu farauta da karnukansu su shiga daji. Sun tafi farautar kuma sun kamo namun daji masu yawa kuma karnukan ne suka kama mafi yawa daga cikin namun dajin. Alara ya aike wa Sarkin Oyo wasu daga cikin namun dajin da aka yi farautar kuma aka dafa sauran naman a fadar Alara aka sha biki. Da aka gama cin naman sai aka tara kasusuwa aka bawa karnuka. Daya daga cikin karnukan ya fusata kan cewa kasusuwa kawai aka basu. An ce karen ya yi magana irin ta 'yan adam inda ya koka cewa su ne suka koma dabobin amma kasusuwa kawai aka ba su. Da mahautan su ka yi yunkurin kashe wannan karen sai ya bace bat. Tun daga wannan lokacin aka haramta alaka da karnuka a garin Ara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel