Mo Salah ya karbi bakuncin Dr. Isa Pantami a filin tashin jirage Masar

Mo Salah ya karbi bakuncin Dr. Isa Pantami a filin tashin jirage Masar

Mun samu labari cewa Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami sun hadu da ‘Dan kwallon kafan nan na Duniya, Mohammed Salah.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Nairaland, Ministan kasar ya ci karo da ‘Dan wasan gaban na kungiyar Liverpool ne a babban filin tashin jirgin saman Cairo da ke kasar Masar.

Hotuna sun nuna cewa Ministan da ‘Dan wasan sun gana ne a wani daki da ake warewa manyan baki a filin jirgin. Hakan ya zo daidai lokacin da Salah ya zo gida domin bugawa kasarsa.

‘Tauraron ‘Dan wasan da ke buga kwallo a kasar Ingila ya dawo Afrika ne da niyyar taimakawa kasar Masar zuwa gasar cin kofin Nahiyar da za a buga a cikin shekarar 2021 mai zuwa.

KU KARANTA: Buhari ta yi wa Maza huduba su yi koyi da Annabi a Ranar Mauludi

Mo Salah ya karbi bakuncin Dr. Isa Pantami a filin tashin jirage Masar
Dr. Isa Ali Pantami ya na musafaha tare da Mo' Salah
Asali: Twitter

Kawo yanzu dai ba mu da labarin abin da ya biyo da Ministan ta babban Birnin Masar watau Cairo. Kwanakin baya dai ya na cikin Tawagar Najeriya da ta halarci taro a kasar Saudiyya.

Mohammed Salah wanda ya na cikin fitattun Musulman ‘yan kwallon Duniya zai buga wasa da kasar Kenya a Ranar Alhamis dinnan, sannan kuma za su sake karawa a Ranar Litinin.

Ba mu samu rahoton wainar da aka toya tsakanin Ministan na Najeriya da ‘dan wasan Larabawan ba. A hotunan da aka wallafa an gan su tare da Jami’in tsaro da kuma wani mutumi a gefe.

Idan ‘dan wasa Mohammed Salah ya samu isasshen lafiya ya na cikin wadanda Masar ta dogara da su wajen taimaka mata zuwa Gasar AFCON na badi bayan ta sha kunya a kasarta bana.

Mo Salah ya karbi bakuncin Dr. Isa Pantami a filin tashin jirage Masar
'Dan wasa Salah tare da Dr. Isa Pantami ana wata tattaunawa
Asali: Twitter

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel