Shawara: Idan kana taimako, sai Allah Ya kara maka arziki, Inji Aliko Dangote

Shawara: Idan kana taimako, sai Allah Ya kara maka arziki, Inji Aliko Dangote

Fitaccen attajirin Duniya, Aliko Dangote ya bayyana cewa yawancin mutane basu iya taimaka ma talakawa saboda kyashi, amma basu san cewa yawan abin da kake bayarwa, yawan Albarkar da Allah zai maka ba.

The Cables ta ruwaito Dangote ya bayyana haka ne yayin taron gidauniyar Florence Otedola Cuppy daya gudana a babban birnin tarayya Abuja, inda ya gabatar da jawabi a kan muhimmancin taimaka ma gajiyayyu mabukata.

KU KARANTA: Zakaran da Allah Ya nufa da cara: Yan Boko Haram sun sako wani limamin coci da dalibar makaranta

Gidauniyar ta shirya taron ne domin tara kudaden da za’a yi amfani dasu wajen kulawa da yara maars galihu a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, inda a yayin taron Dangote ya bayar da kyautar naira miliyan 100.

“Ina sane da cewa mun yi sanadin da yasa wasu yan Najeriya sun fara taimaka ma marasa galihu, Najeriya ta yi mana riga da wando, don haka duk da yawan bukatunmu, akwai bukatar mu ma mu bada namu gudunmuwar, kada mu jira sai gwamnati ta yi mana komai.” Inji shi.

Haka zalika Dangote ya jinjina ma abokinsa Femi Otedola bisa gudunmuwar naira biliyan 5 daya baiwa gidauniyar, inda yace wannan ya nuna Otedola ba wai mai kudi bane kawai, shi ma ya shiga sahun masu arziki.

“Femi ya bayyana ma duniya ya zama mai arziki yanzu ba wai mai kudi ba kawai, a yanzu ya zama mai arzikin da baya cin kudinsa shi kadai da iyalansa, ta tabbata yana taimaka ma mabukata. Ni dai daman a sha fada cewa zan rabar da yawancin dukiyana kafin na mutu, kun san dole ne zamu mutu wata rana.” Inji shi.

Daga karshe Dangote ya jinjina ma Cuppy saboda jajircewar da ta nuna wajen ziyarar data kai garin Maiduguri don ganin halin da yaran suke ciki, a cewarsa ya gayyaci mutane da dama zuwa Borno daga Legas amma basa zuwa, sai ga shi Cuppy ta bi shi sun tafi Borno har ma ta yi wasa da yaran.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel