Daukaka guda da marigayi Murtala ne kawai ya samu a cikin tsoffin shugabannini mulkin soji Najeriya

Daukaka guda da marigayi Murtala ne kawai ya samu a cikin tsoffin shugabannini mulkin soji Najeriya

Har a yau, naira ashirin kadai ce kudin Najeriya da ke dauke da hoton tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soji. Shugaban kuwa shine janar Muratala Ramat Muhammed.

An haifi Murtala Muhammed ne a ranar 8 ga watan Nuwamba 1938 a Kurama quarters a Kano, Najeriya. An haifesa ne a tsaso na fulani kuma gidan alkalai domin kuwa mahaifin kakansa da kakansa sun rike sarautar shugaban alkalan Kano.

Tsohon shugaban kasar na da dangantaka da Aminu Kano, Aminu Wali da sauran iyalan Walin Kano. Ya samu karatun farkon rayuwarsa a Cikin Gida Elementary School wacce take cikin masarautar Kano. Ya koma makarantar firamare ta Makama da ke Kano wacce take wajen masarautar. Ya koma kwalejin Rumfa a 1949 kafin daga bisani ya koma shahararriyar kwalejin Barewa da Zaria inda ya samu shaidar kammala sakandirensa a 1957. A shekarar kuma ya nemi gurbi a rundunar sojin Najeriya.

Murtala ya shiga aikin soja ne a shekarar 1958. An fara horar dashi a Najeriya da Ghana inda daga baya ya wuce Sandhurst Royal Military Academy da ke Ingila a matsayin dalibin soja. Ya samu horarwa a Carrerick Garrison inda a 1961 ya fada aikin sojin tsundum.

DUBA WANNAN: Zuwa kotu a keken guragu: Iyalin Maina sun fadi gaskiyar halin da lafiyarsa ke ciki

A ranar 30 ga watan Yuli 1975, Marigayin ya zama shugaban kasar Najeriya lokacin da aka yi juyin mulki ga Janar Gowon. A cikin kankanin lokaci Murtala ya yi suna tare da samun sunan sadauki saboda sabbin dokokinsa.

Murtala ya fara shirye-shiryen gina sabon birnin tarayya. Ya kafa kwamitin da Jastis Akinola Aguda ya jagoranta inda suka zabi Abuja a matsayin sabon birnin tarayya. A ranar 3 ga watan Fabrairu 1979 ne shugaban ya sanar da sabon babban birnin tarayya nan gaba zata koma Abuja. A ranar ne kuma Janar din ya bayyana sabbin kirkirarrun jihohin da suka hada da Bauchi, Benuwe, Barno, Imo, Niger, Ogun da Ondo. A ranar kuma jimillar jihohin Najeriya suka kai 19.

An kashe Murtala yana da shekaru 37 a duniya tare da hadiminsa Laftanal Akintunde Akinsehinwa a ranar 13 ga watan Fabrairu 1976 a juyin mulkin da Laftanal kanal Buka Suka Dimka ya jagoranta.

Makami daya da ke hannunsu shine bindigar fiston da mai tsaronsa ke dauke da ita. Hakan ne kuwa yasa kisansa yayi musu sauki. Shugaban ma'aikatansa Olusegun Obasanjo ne ya ne ya gajesa wanda daga bisani ya mika mulki ga farar hula a ranar 1 ga watan Oktoba 1979.

A yau, hoton jarumi Murtala ya kawata naira ashirin kuma filin tashi da saukar jiragen sama na Legas ne aka gina da sunansa don tunawa dashi.

Janar Murtala ya rasu ya bar matarsa daya Ajoke. Suna da 'ya'ya shida. Aisha, Zakari (ya rasu) Fatima, Abba ( wanda ake kira da Risqua) Zeliha da Jummai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel