Tirkashi! Ma'auratan da suka fi kowa tsufa a duniya sun shiga littafin tarihin duniya

Tirkashi! Ma'auratan da suka fi kowa tsufa a duniya sun shiga littafin tarihin duniya

- Wasu ma'aurata masu shekaru 80 da aure mazauna birnin Texas a USA sun shiga littafin tarihin duniya

- Ma'auratan sun yi aure ne tun a shekarar 1939 bayan da suka hadu a jami'ar Texas

- A halin yanzu John na da shekaru 106 inda Charlotte ke da shekaru 105 a duniya

John Henderson mai shekaru 106 tare da matarsa Charlotte mai shekaru 105 da ke Texas a USA sun shiga littafin tarihin duniya a matsayin ma'auratan da suka fi dadewa a duniya.

A ranar 15 ga watan Disamba ne zasu shekara 80 da aure.

Sun hadu ne a jami'ar Texas a shekarar 1934 inda Charlotte ke karatun zama malamar makaranta shi kuwa John na gadin kungiyar kwallon kafa.

Masoyan sun yi aure ne a shekarar 1939 kuma sun kashe dala bakwai ne a dakin otal din da suka yi amarcinsu.

DUBA WANNAN: Ire-iren abinci 5 da ya kamata dan adam ya guda kafin kwanciya barci

A takaice dai, John ne tsohon dan kwallon kafa na UT da ke da rai a yanzu kamar yadda CNN ta sanar.

A shekaru 84 da suka gabata, ya zama al'adar John halartar a kalla wasan kwallon kafa daya a duk shekara.

Dukkansu suna nan garas da lafiyarsu kuma John na fita atisaye kowacce rana. Shekaru goma da suka gabata, ma'auratan sun koma kauyen Longhorn, cikin tsoffin daliban jami'ar Texas.

Menene sirrin tsawon rai da kuma aure mai cike da farinciki?

Rayuwa tsaka-tsaki kuma ka zamo tamkar aboki ga abokiyar zamanka, in ji John.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel