Ghana ta ba 'yan Najeriya dake kasuwanci a kasar wa'adin tattara komatsansu

Ghana ta ba 'yan Najeriya dake kasuwanci a kasar wa'adin tattara komatsansu

An umarci 'yan Najeriya da ke kasuwanci a kasar Ghana da su rufe shagunansu zuwa ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamba, 2019 ko kuma a koresu ta karfi a matsayin maida martani da gwa,natin kasar tayi na rufe iyakokin Najeriya da gwamnatin tarayya tayi.

Kungiyar 'yan kasuwar kasar Ghana da ta masu saida kayayyakin wutar lantarki ne suka bada wa'adin.

Daya daga cikin sanarwar da da aka gani a kasuwar Kumasi dake Ghana kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito shine: "Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!! Kamar yadda dokar cibiyar habaka kasuwanci ta Ghana ta tanadar, bai kamata ku zamo a kasuwar nan ba. A don haka ne muke umartar ku da barin kasuwar nan zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba, 2019. Daga GUTA."

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa na sha kaye a kotun daukaka kara - Tsohon gwamnan APC

Wata sanarwar kuma itace kamar haka: "Jan kunne! Jan kunne!! Jan kunne!!! Yarjejeniyar da ke tsakanin GUTA, GEDA da bakin haure a kasuwanninmu ya zo karshe. A don haka ne muke shawartar bakin haure da su hanzarta barin kasuwanninmu zuwa karshen makon nan ko a fita dasu ta karfi. Daga GUTA da GEDA."

Wani dan Najeriya da ke kasuwanci a kasar Ghana ya sanar da jaridar The Guardian cewa, "Sun rufe wasu daga cikin shagunanmu kuma suna barazanar kara rufe sauran nan da 14 ga watan Nuwamba. Sun fusata ne sakamakon rufe iyakokin Najeriya da akayi wanda ya shafi kasuwancinsu."

"Ana ta barazanar rufe kasuwancin 'yan Najeriya a kasar tare da yunkurin maido 'yan Najeriya gida saboda rashin takardar shaidar aikin yi, karuwanci, damfara da sauran dalilan da suke fada. Sun kara tsadar samu lasisin yin aiki a kasar tare da kara haraji akan kasuwancin 'yan Najeriya don a fusata su." in ji dan kasuwan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel