An zabi Musulmai maza da mata 26 mukaman siyasa a kasar Amurka

An zabi Musulmai maza da mata 26 mukaman siyasa a kasar Amurka

Akalla yan takara musulmai guda 26 aka zaba cikin musulmai 81 da suka fito neman kujerun siyasa daban daban a zaben jahohi da na kananan hukumomi na kasar Amurka daya gudana a ranar Talata, 5 ga watan Nuwamba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata kungiyar inganta alaka tsakanin Musulmai da yan kasar Amurka, Council on American-Islamic Relations, CAIR, ce ta bayyana haka inda tace Musulmai 26 ne suka samu nasara a wannan zabe.

KU KARANTA: Wani mutum mai yara 23 ya yi cinikin dansa a kan kudi naira miliyan 5 a Nassarawa

CAIR ta bayyana cewa a shekarar 2019 gaba daya an samu jimillar yan siyasa musulmai 34 da suka lashe zabuka daban daban a jahohi da kananan hukumomi daban daban na kasar Amurka, inda tace daga cikinsu akwai mata gud 16.

“Wannan nasarori sun nuna cewa musulman kasar Amurka sun fara shiga ana damawa dasu a sha’anin mulki a kasar Amurka, Musulman kasar Amurka suna shiga zabe ne saboda yawancinmu muna sane da cewa akwai gudunmuwar da za mu bayar wajen gyaran ilimi da kiwon lafiya.

“Me ya kamata Musulman kasar Amurka su yi a lokacin da ake samun yawaitan matsalolin kin jinin addinin Musulunci da Musulmai a karkashin mulkin da ake kyamar baki? Shi ne muna shiga zabe, kuma muna ci.” Inji kungiyar.

Alkalumma sun nuna daga cikin musulmai 26 da suka lashe zaben, 13 daga cikinsu sabbin yanka ne, yayin da sauran 13 kuma sun zarce a mukamansu ne. guda daga cikinsu it ace Safiya Khalid, yar shekara 23 da ta yi takarar kujerar karamar hukumar Lewiston City Council a inuwar jam’iyyar Democrat.

Haka a jahar Virginia, Ghazala Hashmi ta zamto Musulma mace ta farko da ta fara shiga majalisar dattawan jahar, ita ma Nadia Mohamad ta zamto Musulma mace ta farko da aka fara zaba a majalisar karamar hukumar St. Louis Park, Minn.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel