2020: Buhari ya tsayar da ranar bude iyakokin Najeriya

2020: Buhari ya tsayar da ranar bude iyakokin Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da kara tsayin wa'adin atisayen da aka yi wa lakabi da 'Exercise Swift Response' wanda ya jawo aka rufe iyakokin Najeriya na kasa da makwabatan kasashe.

An rufe iyakokin Najeriya ne tun ranar 20 ga watan Agusta, kuma ana saka ran bude iyakokin a ranar 31 ga watan Janairu, sabanin tsammanin da wasu ke yi na cewa za a bude iyakokin kafin lokacin bikin Kirsimeti domin 'yan kasuwa a yankin kasashen Afrika ta yamma su samu su sarara.

A cikin wata sanar wa mai lamba kamar haka: NCS/ENF/ABJ/221/S.45 mai dauke da sa hannun Victor David Dimka, shugaban sashen tilasta biyayya ga dokokoki a hukumar Kwastam, ya ce sun samu takardar neman su yi biyayya ga umarnin dakatar da atisayen daga ranar 31 ga watan Janairu. An fitar da takardar sanarwar ne ranar 1 ga watan Nuwamba, 2019.

"An umarce ni na sanar da ku cewa duk da an samu gagarumar nasara ta fuskar tsaro da tattalin arziki sakamakon rufe iyakokin Najeriya na kasa, har yanzu akwai wasu manufofi da gwamnati ke son ta cimma.

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Kungiyar 'yan kasuwan Ghana ta rufe shagunan kasuwancin 'yan Najeriya

"A saboda haka ne shugaban kasa ya amince da kara tsawon wa'adin atisayen da ake yi zuwa ranar 31 ga watan Janairu, 2020.

"Ana bukatar dukkan hukumonin tsaro da su sanar da jami'ansu, dake cikin aikin atisayen, wannan sabon canji da aka samu.

"Za a biya dukkan jami'an da ke cikin atisayen kudinsu na alawus da zirga-zirga na tsawon wa'adin da aka kara ba tare da wani bata lokaci ba," kamar yadda yake a cikin sanarwar.

A ranar 20 ga watan Agusta ne shugaban hukumar kwastam, Hameed Ali, ya sanar da fara atisayen "Exercuse Swift Response" wanda ya kunshi dakarun soji da sauran jami'an hukumomin tsaro na ksa domin kawo tsafta da gyara a kan iyakokin Najeriya na kasa da ake amfani da su wajen shigo da kayan da dokar kasa bata amince da shigo wa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel