Amfani 10 da ganyen lansuru ke da shi a jikin dan Adam

Amfani 10 da ganyen lansuru ke da shi a jikin dan Adam

Wani kwararren Likita da ya shahara wajen sanin ilimin sinadirai dake cikin ganyayyaki, Paul Okoh, ya yi kira ga mutane da su lazumci cin ganyen lansuru.

A cewarsa ganyen na dauke da sinadirai dake hana kamuwa da cututtuka sannan da kara karfin garkuwar jiki.

Dakta Okoh yace ganyen lansuru na dauke da sinadarin ‘Beta-carotene da Vitamin C’ wanda ke taimakawa wajen warkar da ciwo a jiki, ciwon sanyin kashi ‘Arthritis’, daji da sauran su.

Akan hada ganyen lansur a cikin abinci kamar shinkafa, faten dankali, faten tsaki da kuma sauran su sannan aka ci wannan ganye danye ko kuma a kwatanta shi da kuma garin kuli-kuli wanda likitoci suka ce yin haka ya fi karfafa garkuwan jiki.

KU KARANTA KUMA: Tikashi! Kwarto ya ziyarci dakunan kwanan dalibai mata a jami’ar ABU (bidiyo)

Ga amfani 10 da ganyen lansuru ke dauke da shi:

1. Cin ganyen lansur na gyara fatar mutum. Lansuru na maganin Kyasfi dake kama fata. Ana nika shi a hada da man da ake shafawa ko kuma da ruwa a shafa a jiki. Yana gyara fata sosai.

2. Cin Ganyan lansuru na maganin cutar ido.

2. Yana maganin hawan jini.

3. Ganyen na kawar da ciwon zuciya.

4. Cin ganyen Lansuru na kawar da laulayin da mata kan ji idan suna jinin al’ada.

5. Yana warkar da rauni ko ciwo a jikin mutum.

6. Yana warkar da rauni ko ciwo a jikin mutum.

7. Cin Ganyen lansur na kawar da warin baki.

8. Ganyen na kara jini.

9. Yana rage kiba a jiki.

10. Yana kara karfin namiji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng