Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ya barke bayan wani direba ya kashe mata uku 'yan gida daya

Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ya barke bayan wani direba ya kashe mata uku 'yan gida daya

Zanga-zanga ta barke a garin Uselu da ke babban tittin Benin-Legas a ranar Asabar bayan wani direba ya kashe wasu 'yan mata 'yan gida daya su uku a hanyarsu ta zuwa sabuwar kasuwar Benin.

Wata mata da ke raka 'yan matan zuwa kasuwa ita ma ta mutu.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 6.15 na safiyar yau Asabar.

Direban motar kirar BMW da matarsa sun makale cikin motar bayan motar da shige cikin wani magudanan ruwa a gefen titin.

Ba a san sunnan direban ba a lokacin da ake hada wannan rahoton.

Matasan Uselu sun fita tittuna suna zanga-zanga inda suke rufe babban titin.

DUBA WANNAN: Ban iya magana da harshen hausa sosai ba - Zahra Buhari

Hanyar ce ta bulle zuwa Jami'ar Benin inda za a gudanar da bukin Al'addu na Kasa (NAFEST) na 2019.

Wani mazaunin garin, Osas Ikpomwosa ya ce sun farka ne kawai sun tarar da gawarwakin mutum hudu a titin.

Osas ya ce daya daga cikin wadanda aka kashe tana dauke da juna biyu.

Ya ce 'yan sanda ne suka zo suka ceto mutumin da matarsa a cikin motarsu da ta makale a magudanan ruwan.

Osas ya ce sun kuna wuta a titin saboda 'yan sandan sun zo suna korar masu zanga-zangar har suna harbinsu da bindiga.

Ya ce 'yan sandan sun harbe mutane hudu cikin masu zanga-zangar kuma sun tafi da su.

Ya ce, "Hatsarin ya faru ne misalin karfe 6 na safe kusa da tashar motar Uselu inda wani mutum da matarsa suka buge mata hudu.

"Gawar daya daga cikin matar yana cikin magudanan ruwa yayin da sauran ukun suna kan titi. Mota kirar BMW ce ta buge su. 'Yan sanda sun zo sun ceci mutumin da matarsa da suka yi rauni.

"Daga bayan 'yan sanda sun dauke gawarwakin. Sun dawo sun ce mana za su cigaba da bincike kan lamarin. Kawai sai suka fara harbe-harbe. Mun rufe titin ne saboda 'yan sandan sun tafi da wasu 'yan uwan mu."

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwabuzor ya ce abin bakin ciki ne.

Ya ce jami'an 'yan sanda sun garzaya wurin da abin ya faru domin tabbatar da doka da oda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel