Ministan sadarwa ya dau wani mataki na musamman ga kamfanonin sadarwar wayar hannu

Ministan sadarwa ya dau wani mataki na musamman ga kamfanonin sadarwar wayar hannu

Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami ya umarci hukumar NCC da ta hukunta duk kamfanin sadarwar da aka samu da laifin cirewa masu amfani da layukansu kudi ta hanyar da ta saba ka’ida.

Jaridar Premium Times ta ruwaito mana cewa, mai magana da yawun bakin ministan, Uwa Suleiman ce ta aiko mata da wannan labarin a ranar Alhamis 24 ga watan Oktoba, 2019.

KU KARANTA:Kotu ta daure wani mutum a gidan yari bayan ya yiwa yara 2 fyade

Pantami ya dakatar da shirin cire kudin da suka shafi USSD daga dukkanin kamfanonin sadarwa na wayar salula a Najeriya. Saboda cire kudin abu ne wanda ya sabawa doka.

Da yake martani ga koken jama’a bisa wannan yinkuri na kamfanonin sadarwa a shafinsa na Twitter, Pantami ya ce bai da masaniya game da shirin kamfanonin na cirewa mutane kudi ta hanyar USSD.

“Mun bai wa hukumar NCC umarnin ta fadawa MTN cewa ta dakatar da wannan shirin nata. Bamu samu labarin wannan tsarin ba a hukumance daga kamfanin sadarwar. Za kuma muyi bincike domin daukan matakin da ya dace a kai.” Inji Ministan.

Ministan ya cigaba da cewa, akwai korafe-korafen da jama’a suka yi na cewa, tun tuni kamfanin MTN ya soma cire masu wannan kudin da zarar sun sanya kudi daga bankinsu zuwa cikin wayarsu.

“Wannan sanarwar tamkar tunatarwa ne ga jama’a, idan har akwai wanda aka cire masa kudi kuma ya tabbata ya na da cikakkiyar shaida to ya garzaya zuwa hukumar NCC domin daukan matakin da ya dace.” Inji Pantami.

Har ila yau, Ministan ya yi magana da kakkausar murya inda ya ce, babu yanda za ayi gwamnati ta zuba ido tana goyon bayan rashin gaskiya. A don haka dole a dauki wannan doka da muhimmanci.

https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/359301-communications-minister-orders-ncc-to-sanction-culpable-mobile-operators-on-ussd-service-charge.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel