Sanatan Kaduna ya sha alwashin fallasa karin cibiyoyin horar da kangararru da basa bisa ka’ida

Sanatan Kaduna ya sha alwashin fallasa karin cibiyoyin horar da kangararru da basa bisa ka’ida

Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Uba Sani ya sha alwashin kaddamar da aikin tona dukkanin haramtattun cibiyoyin horar da kangararru a kasar.

Sanatan yace zai gabatar da wata doka don kula da tsarin kafa cibiyoyin horar da kangararru a Najeriya, wanda zai magance lamarin kafa haramtattun cibiyoyi da kuma tabbatar da bin hanyoyin da suka fi dacewa wajen gudanar da ayyuka.

Sanatan a jawabinsa yace bayyanar wasu “cibiyoyin horo” a Rigasa, karamar hukumar Igabi da Zaria wanda suka kasance abun damuwa a zukatan yan Najeriya da kuma al’umman kasashen waje abun kaico ne.

Yace yayin da akwai muhimmanci da kuma bukatar gaggauta rufe haramtattun cibiyoyin horar da kangararru, dole masu ruwa da tsaki su hada kai don kafa tsarin da zata tabbatar da cibiyoyin horar da kangararru na halal.

KU KARANTA KUMA: An kama wani fasto kan zargin garkuwa da mutum a Nasarawa

Ya bayyana cewa hakan zai taimaka ma hukumomin da za su lura da lamarin wajen tantance haramtattun ciboyoyin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel