Gwamnatin Yobe ta farfado da wani katafaren kamfanin dake jihar

Gwamnatin Yobe ta farfado da wani katafaren kamfanin dake jihar

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya tayar da kamfanin sarrafa buhu wanda ya kai shekaru takwas baya aiki bayan da aka rufe shi.

Kamar yadda kakakin gwamnan, Abdullahi Bego ya fadi, wannan shi ne kamfani na uku da gwamnatin ta tayar a Yobe. Sauran guda biyun su ne; Kamfanin fulawa na Yobe da Kamfanin sarrafa karfen Aluminium.

KU KARANTA:Allah ya yiwa Muhammadu Dan Madami, Sa’in Katagum rasuwa

Janar manaja na kamfanin buhun, Engr Shuaibu Gadaka ya ce an sanya sabbin kayan aiki a kamfanin domin cigaba da aiki gadan-gadan.

Ya kuma kara fadin cewa, nan da makonni biyu za a soma kawo kayan aiki domin shiga cikin ainihin aikin da kamfanin keyi na sakar buhu.

Gadaka ya yi karin bayani a kan kudin da Gwamna Buni ya kashe domin tayar da kamfanin sakar buhun. An riga da an tanadi kayayyakin aiki da kamfaninke bukata, abinda kawai ya rage yanzu shi ne a fara saka buhu.

A wani labarin kuwa mai kama da wannan za ku ji cewa, Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya zabi kwamishinoni 23 a ciki har da dan gidan Atiku Abubakar wato Adamu Atiku.

Gwamna Fintiri ya mika sunayen kwamishinonin ne ga majalisar Adamawa ranar Laraba 23 ga watan Oktoba, 2019. Jerin sunayen na zuwa majalisar ne bayan kwana daya kacal da majalisar ta aminta da nadin masu bai wa gwamnan shawara su 40.

https://www.dailytrust.com.ng/yobe-woven-sacks-factory-back-in-operation.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel