Fintiri ya zabi dandan Atiku da wasu mutum 22 a matsayin kwamishinoninsa

Fintiri ya zabi dandan Atiku da wasu mutum 22 a matsayin kwamishinoninsa

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya aikawa majalisar jihar Adamawa da sunayen zababbun kwamishinoninsa 23.

Daga cikin jerin sunayen akwai sunan yaron Atiku Abubakar dan-takarar shugaban kasar PDP a zaben 2019, wato Adamu Atiku.

KU KARANTA:Alkalai mutane ne kamar kowa, saboda haka za su iya yin kuskure – Jastis Tanko

Jerin sunayen kwamishinonin ya iso majalisar ne tare da wata wasika wadda Gwamna Finitiri ya aiko da ita zuwa ga majalisar ranar Laraba 23 ga watan Oktoba.

Aminu Iya, Kakakin majalisar Adamawa ne ya karanto wasikar tare da fadin sunayen mutanen da Gwamna ya aiko da su.

Daga cikin mutanen da sunansu ya fito akwai: Mustapha Musa Jika (Yola ta kudu), Ibrahim Yayaji Mijinyawa (Yola ta arewa), Umar Iya Daware (Fufore), Shuaibu Audu (Mayo Belwa), Sanusi Faruk (Toungo), Elijah Tumba da John Dabari duk daga Michika.

Har ila yau, akwai Muhammad Umar (Madagali), Sunday Mathew (Mubi ta arewa), Farfesa Isa Abdullahi (Mubi ta kudu), Hassan Kaigamma (Maiha), Dr Umar Garba (Hong), Lami Patrick (Gombi), Usman Yahaya Diyajo (Girei) da Bappa Dalhatu Isa (Ganye).

Sauran kuwa su ne; Mrs Wilbina Jackson (Guyuk), Justina Obadiah Nkom (Lamurde), Iliya James (Demsa) da kuma Adamu Titus (Shelleng).

Bayan ya kammala fadin sunayen kwamishinonin, Kakakin majalisar ya umarci kwamitin majalisar da alhakin tantancewar ya shafesu da su soma shirya abu na gaba.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, a ranar Talata 22 ga watan Oktoba ne majalisar ta amince da nadin masu ba gwamnan shawara su 40.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel