Da zafinsa: Yarinyar da ta kona kanta a kan a hanata auren saurayinta a Zamfara ta rasu

Da zafinsa: Yarinyar da ta kona kanta a kan a hanata auren saurayinta a Zamfara ta rasu

Aisha ‘yar shekara 17 a duniya wadda ta kunna ma kanta wuta jihar Zamfara sakamakon an hanata auren saurayinta ta rigamu gidan gaskiya ranar Laraba 23 ga watan Oktoba.

Mallam Aminu Muhammad mahaifin yarinyar ne ya shaidawa Daily Trust labarin rasuwar diyar tasa. Ya ce, yarinyar ta rasu ne asibitin Federal Medical Centre dake Gusau a safiyar Laraba.

KU KARANTA:Ku tsaya a matsayin da aka sanku a zaben 2023, Jega ya roki INEC

Mahaifin ya bayyana labarin rasuwar yarinyar inda ya ce sun jima suna fama da kudin maganinta bayan an kwantar da yarinyar a asibiti kwanaki 45 da suka wuce.

Aminu ya ce: “Jikinta gaba dayansa rufe yake da bandeji inda aka tafi da ita dakin wanka domin sanya mata sabon bandejin.

“Dawowarta daga dakin wankan ke da wuya sai tace ga garinku nan. Mun jima muna fama da kudin magani tun daga ranar da aka bamu gado wannan asibitin yau kwana 45 kenan. Ko kwana biyu da suka wuce an rubuta mana maganin naira 26,000 bamu samu siya ba saboda ba kudin.

“Hakika mun samu gudunmuwa daga wurin jama’a da dama. Kuma mun kashe N700,000 a zaman jinyan da mukayi wanda kuma akasarin kudin daga gudunmuwa muka samesu. Kunar dake jikinta na da yawa sosai.” Inji mahaifin yarinyar.

Idan baku manta ba dai, a farkon watan Satumbar 2019 ne Aisha wadda ke zaune a shiyar Albarkawa dake Gusau ta bankawa kanta wuta saboda an hana sauriyanta ya aurenta kasancewar bai da tsayayyar sana’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel