Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)

Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)

Shi dai wannan matashin mai suna Ezra Suwanta Zako an haife shi ne kamar ko wane yaro, inda ya soma girma kamar yadda duk wani jariri ke girma. Sai daga baya ne girman nasa ya fara bambanta da na sauran yara.

Shekarar Ezra shekara 26 yanzu, sannan kuma saboda tsawon da Allah ya bashi ana yi masa lakani da Dogo. Ezra dai tsawonsa ya kai kafa bakwai, hakan ya sanya ake ganin a jihar Kaduna gaba daya babu wanda ya kai tsawonsa.

Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)
Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)
Asali: Facebook

KU KARANTA:Gwamna Bala Mohammed ya nada Ma’aji Misau shugaban ma’aikatan Bauchi

A lokacin da wakilin jaridar Arewa Trust Weekly ta kai ziyara kauyen Dusai inda a nan ne Ezra yake da zama sai ta same shi tare da mahaifinsa Suwanta Zako mai shekaru 80.

Kauyen nasu na Dusai yana nan a tsakanin Kagoro da Manchock cikin karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna. An haifi Ezra ne a watan Nuwamban 1992 kuma shi ne na hudu a cikin yaran mahaifinsa dake raye a yanzu.

Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)
Ezra Suwanta Zako: Mutum mafi tsawo a jihar Kaduna (Hotuna)
Asali: Facebook

Ezra ya fito ne daga tsatson wani shahararren mafarauci wato Katagwan wanda ya zauna a Kagoro kimanin shekaru 300 da suka wuce. Ezra dai tsawonsa ba tsintarsa yayi ba, saboda kakan nasu wato Katagwan shi ma an bayyana a matsayin mutum mai matukar tsawo sosai.

A wata ‘yar takaitacciyar hira da Ezra yayi da Arewa Trust ya ce a lokacin da ya soma yin tsawo sosai, abin ya fara damunsa saboda tsokanarsa da yara keyi musamman a makaranta.

Amma kuma hakan bai sanya shi ya damu ba, kasancewar ya fito daga babban gida wato gidan Katagwan, fitaccen mafarauci kuma jarumi a Kagoro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel