Ke duniya: An kama wani saurayi da kan wata kyakkyawar budurwa a cikin leda

Ke duniya: An kama wani saurayi da kan wata kyakkyawar budurwa a cikin leda

- An kama wani saurayi dauke da kan wata kyakkyawar budurwa a cikin leda

- Bayan kama shi an tilasta shi akan sai ya fito da abinda ke cikin ledar, yana fitowa dashi aka ga kan mutum ne

- Tun kafin ya yanke kan budurwar ashe dama ta dauki hoto ta sanya a shafinta na sada zumunta, yana fito da kan nata ba wuya mutane suka gane ta

Wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sadarwa na zamani ya bayyana yadda wani saurayi ya shiga hannun jami'an tsaro bayan an kama shi da ya yanke kan wata budurwa ya sanya a cikin leda.

Bayan jami'an tsaron sun kama shi sun tilasta shi akan ya fito da abinda ke cikin ledar, bayan ya fito dashi aka ga ashe kan wata budurwa ce.

Ashe kafin mutumin ya kashe budurwar ta sanya hotunan ta a shafukan sadarwa, domin kuwa a lokacin da ya fito da kan budurwar an ganta da irin gashin da ta saka a lokacin da ta dauki hoton.

Ke duniya: An kama wani saurayi da kan wata kyakkyawar budurwa a cikin leda
An kama wani saurayi da kan wata kyakkyawar budurwa a cikin leda
Asali: Facebook

KU KARANTA: An samu naira miliyan 324 a asusun bankin wata mabaraciya

Wani mutumi mai amfani da shafin Twitter ya wallafa wani rubutu akan wannan lamarin, inda yake cewa:

"Yanzu na ga wani bidiyo na wani saurayi da aka kama da kan budurwa a leda.

"Kamata yayi a kashe mutumin nan bainar jama'a, a sanya jami'an tsaro su harbe shi kowa ya gani.

"Kawai ka kashe diyar wani saboda kawai kana so sai kayi arziki ko ta halin kaka."

A watannin da suka gabata mun kawo muku rahoton yadda aka kama wani saurayi a garin Abuja dauke da kayuwan kananan yara da yake kamawa yana yankawa yana kaiwa maigidansa yana saya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel