Ahmed Aliyu da jam'iyyar APC sun daukaka kara akan hukuncin zaben jihar Sokoto

Ahmed Aliyu da jam'iyyar APC sun daukaka kara akan hukuncin zaben jihar Sokoto

- Ahmed Aliyu, dan takara kujerar gwamnan jihar Sokoto karkashin jam'iyyar APC da jam'iyyar APC sun daukaka kara

- Idan zamu tuna, a farkon watan Oktoba din nan ne kotun sauraron kararrakin zabe tayi watsi da karar Ahmed Aliyu da APC

- Hakan kuwa shi ne ya jaddada nasarar Gwamna Aminu Wamakko na jihar Sokoto

Dan takarar jam’iyyar APC a zaben kujerra gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu da jam’iyyar APC sun daukaka kara sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe .

A ranar Laraba ne Ahmed Aliyu da jam’iyyar APC suka dauka karar.

Daya daga cikin mambobin kungiyar lauyoyin jam’iyyar, Barista Bashir Jodi, ya bayyana hakan ga wakilin jaridar Punch a Sokoto.

KU KARANTA: Sabon salo: 'Yan sanda sun bukaci wata budurwa da ta nuna rasit din siyan karenta

Idan zamu tuna, a farkon watan Oktoba din nan ne kotun sauraron kararrakin zabe a Abuja ta kori karar da Ahmed da jam’iyyar APC ta kai kotun sauraron kararrakin zabe. Hakan kuwa ne jaddada nasarar dan takarar jam’iyyar PDP, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal.

A sakamakon cigaban da aka samu a yau Laraba, Aliyu da jam’iyyar APC suna bukatar hukuncin karamar kotun daukaka kara ta jihar Sokoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel