Wasu mabiya sun ja shugaba a kasa akan rashin cika alkawari

Wasu mabiya sun ja shugaba a kasa akan rashin cika alkawari

- Wata kungiyar masu zanga-zanga a Mexico sun kama shugaba Hernandez tare da dauresa a mota inda suka ja shi a kasa

- Mutanen sun zargi shugaban ne da rashin cika alkawurran da ya daukar musu yayi yakin neman zabe

- Fusatattun mutanen, sun je har ofishinsa ne inda suka fito dashi ta karfin tsiya daga ofishinsa

Wata kungiyar masu zanga-zanga a ranar Laraba sun daure shugaban Las Margaritas a bayan mota inda suka ja shi a titunan birnin sakamakon rashin cika alkawurran zabe.

El Heraldo de Mexico ne suka bada rahoton cewa masu zanga-zangar sun ja shugaba Jorge Hernandez ne a Chiapas da ke kudancin Mexico.

An sanar cewa, fusatattun masu zanga-zangar sun cigaba da jan Hernandez a kasa ne har zuwa lokacin da 'yan sanda suka zo tare da tare motar da suka dauresa suka kuma kwancesa.

KU KARANTA: Hotunan bikin wata kyakyawar gurguwa da angonta sun jawo cece-kuce a arewa

Shugaban ya samu kananan raunika inda sa'o'i bayan aukuwar lamarin yayi jawabi.

Kamar yadda kafar yada labaran ta ce, masu zanga-zangar sun je har ofishin Hernandez ne inda suka fito dashi ta karfi saboda suna zarginsa da kin cika musu alkawurran da ya dauka lokacin zabe.

Alkawaurran sun hada da, yi musu tituna, jawo ruwan sha da wutar lantarki.

Jami'an tsaron birnin sun zargi fusatattun masu zanga-zangar da yunkurin garkuwa da shugaban inda aka kama akalla mutane 30 tare da raunata 20.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel