Yawan ‘yan Najeriya cikas ne ga cigaban kasar – Sarkin Kano

Yawan ‘yan Najeriya cikas ne ga cigaban kasar – Sarkin Kano

-Sarki Lamido ya kushe yawan mutanen Najeriya inda ya ce matsala ne ga kasar ba jari ba

-Sarkin Kano yayi wannan furucin ne a wurin wani taron tattalin arziki da aka gudanar a Abuja ranar Litinin

-Gwamna jihar Ekiti, Kayode Fayemi da Bishop Mathew Kukah na daga cikin mutanen da suka halarci taron

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi Lamido na II a jiya Litinin 7 ga watan Oktoba ya ce adadin mutanen dake Najeriya nakasu ne ga cigaban kasar.

Sarkin yayi wannan furucin ne a wurin taro karo na 25 a kan tattalin arzikin Najeriya wanda ake gudanarwa a babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA:Nima an nemi yin lalata da ni a yayin da na ke jami'a, inji matar gwamna Fayemi

Taron na tattalin arziki ya samu halartar babban malamin addinin kirista, Bishop Mathew Kukah da kuma Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

Haka zalika taron ya tattauna ne a kan yadda za a dada fito da sabbin hanyoyin bunkasa kasuwanci ta yadda zai kasance mutane za su iya gudanar da shi cikin tsanaki.

Sarkin ya ce, yawan mutanen dake Najeriya nakasu ne ga cigaban kasar saboda har yanzu babu wani abu na amfani da yawan mutanen ke kawowa kasar.

Sanusi ya kara da cewa, akasin abubuwan cigaba yawan ke kawowa kamar su, garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin makiyaya da manoma da kuma ta’addancin ‘yan bindiga.

Sarki Lamido ya ce: “Mutane da daman a maganar cewa yawan tamkar jari ne mai tsoka ga kasarmu, amma sai dai kash har yanzu bamu kai wannan matakin ba. A halin yanzu zai iya cewa yawan mutanen kasar nan matsalace babba a garemu saboda banda yawaitar ayyuka marasa kyau babu abinda yawan ke haifarwa.”

http://community.thenationonlineng.net/forum/nigeria-s-population-a-liability-sanusi

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel