An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai shekaru 29 da ke yin shiga irin ta mata a matsayin karuwa domin ya damfari maza masu zuwa kulob a Legas.

'Yan sanda sun kama Victoe Monday ne a sakamakon kama shi da su kayi yana tsaye a bakin titin Ogunmokun Street sanya da kayan mata misalin karfe 12 na dare yana jirar wanda zai zo ya yi masa tayi.

An ajiye shi a bayan kanta tare da mata ne kafin daga bisani wani dan sanda ya gano ashe na miji ne. Gemunsa ne ya fara tona masa asiri sai kuma aka gano ya sanya gashi na karya ne da kwalliyar fuska da nonuwa na karya.

Majiyar 'yan sanda ta ce Monday ya bayyana cewa rashin aikin yi ne ya jefa cikin wannan mummunan aikin kamar yadda Linda Ikeji's Blog ta ruwaito.

Majiyar ta ce, "Ya kan je kulob ne domin neman maza da za su kwana tare yayin da ya ke sanya da kayan mata. Zai yi ta rawa ne janyo hankali har sai ya samu wanda ya yi masa tayi.

An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)
An kama wani gardi da ya yi basaja a matsayin karuwa yana damfarar maza (Hotuna)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram suna can suna kone gidajen al'umma a Chibok

"Ya kan fara karban wani kaso cikin kudin da za a biya shi na karuwancin ya dan kashe. Yayin da suke shan giya da shakatawa sai ya fadawa mutumin cewa zai yi fitsari daga nan sai ya sulale ya gudu. Ya ce ya kan samu kaman N7,000 zuwa N10,000 duk dare."

Ya kara da cewa ya fara wannan laifin ne tun shekarar 2018 kuma 'yan sanda sun kama shi amma 'yan cocinsu suka karbo shi beli.

An gurfanar da Monday a gaban kotun Majistare da ke Ogba kan laifuka hudu masu alaka da damfara da yin soja gona.

Sai dai bai amsa laifin ba kuma an bayar da belinsa kan N80,000 da mutum daya da ya tsaya masa sannan alkalin kotun Mrs. M.O. Tanimola da dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 16 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel