Hukumar NDLEA ta damke masu sayarwa ‘yan Boko Haram miyagun kwayoyi a Jalingo

Hukumar NDLEA ta damke masu sayarwa ‘yan Boko Haram miyagun kwayoyi a Jalingo

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA ta sanar damu cewa, ta samu nasarar damke mutane 21 wadanda dillancin miyagun kwayoyi zuwa ga mayakan Boko Haram a Jalingo.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Mr John Achema ne ya bada wannan labari ranar Alhamis 3 ga watan Oktoba, 2019 a Abuja yayin da yake zantawa da kamfnin dillacin labaran Najeriya NAN.

KU KARANTA:Majalisar Tarayya ta kara kasafin 2020 daga Tiriliyan 10.002 zuwa 10.729

Mr Achema ya ce an damke wadannan mutanen ne a yayin wani samame da jami’an hukumar tasu suka kai a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

Ya kara da cewa an samu mutanen da nau’uka daban-daban na ganyen wiwi masu yawan gaske, haka kuma akwai kimanin kwalabe 274 na maganin tari wanda aka fi sani da kodin.

Haka zalika, da dama daga cikin mutanen sun amsa laifin nasu ba tare da musantawa ba, inda suka fadi da bakinsu cewa sun jima cikin wannan harkar ta dillancin kwayoyi zuwa ga kungiyar Boko Haram, a cewar Achema.

Achema ya ce: “Uban tafiyar wanda shi ne jagoran masu sayar da kwayoyin ya ayyana rashin aikin yi a matsayin abinda ya jefasu cikin wannan harka.”

“Kimanin katan 153 na tabar wiwi muka samu tare da jagoran tafiyar, kuma a halin yanzu mutum 9 daga cikin 21 suna cigaba da sauraron shari’a a gaban kotun Jalingo yayin da sauran kuwa muke cigaba da gudanar da bincike a kansu.” Inji Achema.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel