Jerin sunaye: Masari ya rantsar da masu bayar da shawarwari na musamman 14

Jerin sunaye: Masari ya rantsar da masu bayar da shawarwari na musamman 14

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya rantsar da sabbin masu bashi shawari na musamman 14 inda ya bukaci su mayar da hankali wurin magance matsalolin al'umma bisa son kai.

A yayin da ya ke jawabi a dakin taron 'yan fadarsa a ranar Laraba, Masari ya ce gwamnatin jam'iyyar APC ta al'umma ce saboda haka dole a mayar da hankali kan magance matsalolin talaka inda ya ce hakan ne yasa ya kirkiri sabbin ma'aikatu domin inganta aikin gwamnati a jihar.

A kan sake nadin masu bayar da shawarar da ya yi, Masari ya ce kwazo da mayar da hankali kan aiki ne yasa ya sake nadu su duk da cewa hudu daga cikin sabbin masu bayar da shawarar suna bukatan lokaci domin gane makamashin aiki.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Babban jami'in tsaron jami'iyyar APC, DSP Adamu ya rasu

"Duk da cewa su sabbin 'yan mazalisar zartawar jiha ne su ba sabbin 'yan jam'iyyar APC bane. An saka su ne wuraren da suka dace," inji shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa sabbin masu bayar da shawarar da aka nada sun hada da: Alhaji Bashir Dayyabu mai bayar da shawara kan hukumomin kasa da kasa masu bayar da tallafi; Comrade Lawal Tanimu mai bayar da shawara kan Kwadago; Alhaji Kabir Sha’aibu mai bayar da shawara kan harkokin siyasa da Abdullahi Ibrahim Mahuta, mai bayar da shawara kan harkokin majalisa.

Wadanda aka sake yi wa nadin sun hada da Muntari Lawal, Bashir Usman Ruwan Godiya, Abdulkadir Mamman Nasir, Hussaini Adamu Karaduwa, Khalil Ibrahim Aminu, Aminu Lawal Jibiya, Lawal Usman Bagiwa, Hamza Muhammad Borodo, Dr Abba Abdullahi, da Abdu Habu Dankum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel