Da duminsa: Jami’ar Ahmadu Bello ta sallami malamai 15 a dalilin laifuka daban-daban

Da duminsa: Jami’ar Ahmadu Bello ta sallami malamai 15 a dalilin laifuka daban-daban

Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) dake Zaria ta sallami malamai guda 15 inda ta ragewa wani matsayi a sakamakon aikata laifukan da suka shafi yin lalata da mata, cin-hanci da kuma halin ko oho da aiki.

A cikin wani daftarin da jaridar Daily Trust ta samu ranar Alhamis wanda ke kunshe da sunayen wadanda aka koran ya nuna cewa malaman dai sun fito ne daga bangarori daban-daban na Jami’ar.

KU KARANTA:Sarkin Dutse ya yabawa gwamnatin Najeriya bisa rufe kan iyaka da ta yi

An tuntubi Daraktan hulda da jama’a na jami’ar, Dr Sama’ila Shehu game da sahihancin labarin, inda ya ce, “tabbas da gaske ne kuma daukar wannan matakin ya zama dole domin ladabtar da malami ko dalibin jami’armu day a kwantanta aikata aiki makamancin wannan.”

Kamar yadda daftarin ya bayyana, kwamitin gudanarwar jami’ar ne ya zartar da wannan hukunci bayan an yi zaman ganawa har sau biyu.

A wani bincike da wakilin jaridar Daily Trust yayi, ya kawo mana labarin cewa wani malamin sashen karantar kimiyyar itace an sallame shi a dalilin neman wata malama mace domin yayi lalata da ita.

Haka kuma wasu malamai uku dake sashen karatun ilimin zamnatakewa, sun rasa aikin nasu ne a dalilin sauya sakamakon jarabawa, cutar da dalibai da kuma bayar da sakamakon jarabawa na bogi.

A karshe jaridar ta tabbatar mana da cewa, da dama daga cikin malaman sun rasa aikin nasu ne a dalilin neman mata dalibai domin suyi fasikanci da su, har wa yau ana cigaba da bincike a kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel