Asibiti sun yi kuskuren zubarwa wata mata da juna biyu a kasar Koriya

Asibiti sun yi kuskuren zubarwa wata mata da juna biyu a kasar Koriya

Wani kwararen Likita ya shiga cikin matsala inda ya yi kuskure wajen aikin zubar da ciki. Wannan Likitan ya yi aiki ne a kan wata mata dabam. Wannan ya faru ne a wani asibiti da ke Koriya.

Kamar yadda Jaridar The Star Online ta kasar waje ta rahoto, jami’an ‘yan sanda sun damke wannan babban Likitan Mata da kuma Unguzomar da ta ke aiki da shi bayan wannan hadari ya auku.

Likitan da yak ware wajen duba Mata ya samu kansa ne cikin matsala bayan gigi ya kai su sun barar da juna biyun mako shida da wata mai ciki ta ke dauke da shi. Wannan ta faru ne a kwanakin baya.

A lokacin da wannan mata ta shiga dakin fida, maimakon Malaman asibitin su duba fuskarta, sai kurum su ka kama bakin aiki. A nan fa su ka zubar mata da ciki bayan sun yi mata allurar da ke sa barci.

KU KARANTA: Dalilan da su ka sa Likitoci ke barin Najeriya zuwa ketare

Likitan ya yi tunanin wata maras lafiya ce yake yi wa aiki wanda ta ke bukatar a zubar mata da cikinta.Wannan ganganci da rashin kula ya sa Malaman wannan asibiti su ka kare a hannun ‘yan sanda.

Da wannan mata ta koma asibiti domin kai kukan cewa ta na samun zuban jini, sai aka tabbatar mata da cewa an zazzage halittar da ke cikin mahaifar bayan ita ainihi magani ta zo nema asibitin.

Babbar matsalar da asibitin da wannan Malamai na ta za su iya fuskanta shi ne a kasar ta Koriya ta Kudu, bai halattta a zubar da ciki ba. Ba dai yau ne Likitoci su ka fara garaje wajen aiki ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel