Hotuna: Yadda wani mutumi ya shiga gida ya iske matar shi kwance da wani kato a kan gadonsu na Sunnah

Hotuna: Yadda wani mutumi ya shiga gida ya iske matar shi kwance da wani kato a kan gadonsu na Sunnah

- Wani mutumi ya bayyana wani abu da ya faru dashi tsakanin shi da matar shi da wani mutumi a shafinsa na Twitter

- Mutumin ya bayyana cewa ya shigo gidan shi sai ya iske matar shi da wani katon gardi kwance suna zina a kan gadon su na aure

- Ya bayyana cewa shekarar su goma suna tare da matar amma a wannan karon ya tabbata cewa sai ya rabu da ita

Wani mutumi ya wallafa wasu hotuna da ya dauka na matar shi wacce suka shafe shekara 10 suna tare a lokacin da ya kamata da wani katon gardi suna zina a kan gadonsu na aure.

Da yake bayyana cewa tabbas yanzu ya dawo zama shi daya, ma'ana zai rabu da matar tashi wacce suka shafe shekaru goma suna tare, mutumin mai amfani da shafin Twitter ya ce tsawon shekaru goma bai taba zama shi daya ba, amma a wannan karon ya san zai ji dadin zaman da zai ba tare da matar tashi ba.

Hotuna: Yadda wani mutumi ya shiga gida ya iske matar shi kwance da wani kato a kan gadonsu na Sunnah
Whites
Asali: Facebook

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: An bude sabon Masallaci na 'Yan Luwadi da Madigo a yankin Turai

Ga abinda mutumin ya ce: "Kwana biyu na dan yi shiru da abubuwa na, ina fuskantar wata babbar matsala da ta shafi rayuwata. Na shigo cikin gidana sai na wuce daki kai tsaye, ina shiga sai na iske matata kwance da wani katon gardi a kan gadonmu na aure, abin ya daure mini kai matuka."

"Sama da shekara goma ban taba zama ni daya ba a rayuwata, amma tabbas na san wannan karon dole zan rabu da ita, kuma na san cewa zan ji dadin zaman da zanyi ba tare da ita ba," in ji mijin.

Hotuna: Yadda wani mutumi ya shiga gida ya iske matar shi kwance da wani kato a kan gadonsu na Sunnah
Whites
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel