NDA: Dalibai 630 ne za a yaye ranar Asabar 5 ga watan Oktoba – Janar Oyebade

NDA: Dalibai 630 ne za a yaye ranar Asabar 5 ga watan Oktoba – Janar Oyebade

Hukumar gudanarwar NDA ta sanar da ranar da za tayi bikin yaye daliban wadanda suka samu horo a fanni daban-daban na soji. Akwai rukunin 66 na sojin kasa, rukunin 67 na sojojin sama da ruwa da kuma rukunin 45 na masu horon a gajeren zango na sojin kasa.

Za ayi wannan bikin ne a ranar Asabar 5 ga watan Oktoba a filin faretin Makarantar Horon Sojojin Najeriya dake Kaduna wato Nigerian Defence Academy wadda aka fi sani da suna NDA.

KU KARANTA:Baya mai goya marayu: Uwargidan gwamnan Zamfara za ta dauki nauyin karatun marayu

Kwamandan makarantar Manjo Janar Adeniyi Oyebade ne ya bada wannan labari a lokacin da yake zantawa ga manema labarai, inda yake fadin yadda bikin na bana zai gudana.

Oyebade ya ce, “A bikin na bana dalibai 630 ne ake tsammanin za a yaye a ranar 5 ga watan Oktoba. Daga cikinsu dalibai 451 za su zamo jami’an sojin kasa bayan kammala bikin.

“A yayin da 89 za su kasance jami’an sojin ruwa sai kuma 90 wadanda za su zamo jami’an sojojin sama, bayan sun kara shekara daya a makarantun rundunoninsa.”

Kwamandan wanda ya samu wakilicin mataimakinsa AVM Ismaila Sadiq Kaita ya ce ana dakon halartar Shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa wurin wannan taro mai muhimmanci.

Ya kuma kara da cewa, za a soma gudanar da shirye-shirye daban-daban wadanda suke dangancin bikin yaye daliban tun daga ranar 14 ga watan Satumba, wanda za a kammala a ranar Asabar 5 ga watan Oktoba.

A wani labarin mai kama da wannan za kuji cewa, uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Balkisu Matawalle tayi alkawarin daukar nauyin karatun marayu a Zamfara.

Uwargidan gwamnan ta fadi wannan maganar ne a wurin taron cika shekaru biyu na kungiyar Juvenile Aid Foundation.

http://leadership.ng/2019/09/18/630-officer-cadets-to-pass-out-from-nda-october-5/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel