Kawata ta nuna tana son mijina, kuma ta sha alwashin raba ni da shi, dan Allah ina mafita - Mata ta nemi shawarar mutane

Kawata ta nuna tana son mijina, kuma ta sha alwashin raba ni da shi, dan Allah ina mafita - Mata ta nemi shawarar mutane

- Wata mata ta wallafa wani rubutu a shafinta na Twitter inda take neman shawara akan wata matsala da take damunta

- Matar ta nemi shawarar ne akan wata kawarta da ta nuna tana son ta kwace mata miji, inda ta nemi ta hada ta dashi

- Matar ta ce ta sha alwashin sai ta kwace shi, sannan kuma ta yi mini barazanar za ta tona asirina akan ina zuwa na karbi kudi a wajen maza

Wata mata ta kai kukan ta zuwa kafar sada zumunta akan wata kawarta da ta nuna tana son mijinta, matar ta nemi shawarar abokananta akan abinda ya kamata tayi akan wannan lamari.

Matar ta wallafa hotuna da suke nuni da irin hirar da tayi da kawarta din wacce ta nemi izininta akan ta bata dama ta nemi mijinta. Matar ta nuna rashin amincewarta inda ita kuma tayi mata barazanar za ta tona mata asiri akan tana zuwa tana tambayar maza kudi.

KU KARANTA: Tirkashi: An kama Aisha Zakari matar da take kiran gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu tana tsorata shi ta wayar salula

Ta mayar mata da martani cewa ai dama mijinta ya san da wannan hali nata na tambayar kudi, saboda haka koda ta fada babu abinda zai faru.

Matar dai ta nemi shawarar wata kawarta ne akan hanyar da za ta bullowa da lamarin, inda ta tura mata hotunan yadda hirarsu ta kaya da mai son kwace mata mijin.

Kawata ta nuna tana son mijina, kuma ta sha alwashin raba ni da shi, dan Allah ina mafita - Mata ta nemi shawarar mutane
Chats
Asali: Facebook

Wannan hotuna da rubutu da wannan mata ta wallafa ya jawo kace nace matuka a shafin sadarwa na Twitter, inda kowa yake fadar albarkacin bakinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel