APC ta dakatar da wani dan majalisar jihar Kebbi
Kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi ya dakatar da Alhaji Habubu Gwandu wanda yake mamba ne a majalisar dokokin jihar Kebbi, bisa zarginsa da laifin yiwa jam’iyya zamba.
Kakakin jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Alhaji Sani Dododo ne ya bayar da wannan sanarwa a cikin wata tattaunawa da yayi da manema labarai ranar Talata 17 ga Satumba a Birnin Kebbi.
KU KARANTA:Najeriya ta samu cigaba a bangaren noma – Bagudu
Sani ya ce: “Kwamitin zartarwar jam’iyyarmu a ranar 16 ga watan Satumba ya aminta da dakatar dakatar da Alhaji Habubu Gwamndu daga APC a dalilin zarginsa da laifin zamba. Mun kafa kwamiti domin soma bincike a kan gaskiyar wannan al’amari.”
Dododo ya kara da cewa, Gwandu ya kasancewa yana halartar ganawa da jam’iyyun adawa a Sokoto da kuma Birnin Kebbi lokuta daban-daban.
“Wannan dakatarwar ta sa na nufin ba zai sake yin wani abu na jam’iyyar APC bat un kuwa daga matakin shiyya, karamar hukuma har zuwa jihad a kasa baki daya.” Inji Sani.
A wani labari makamancin wannan, za ku ji cewa, Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya bayyana irin nasarorin da Najeriya ke samu a bangaren noma.
Gwamnan ya fadi wannan maganar ne ranar Litinin a Damaturu babban birnin jihar Yobe, yayin da ya halarci wani taro na musamman da gwamnatin jihar Yobe ta shirya dangane da harkokin noma.
A cewar Bagudu daga lokacin da Buhari ya zama shugaban Najeriya, noma ya dada bunkasa fiye da yadda abin yake a da. Yanzu Najeriya na iya ciyar da kanta abinda da can bamu iya yinsa, a cewar gwamnan.
https://thenationonlineng.net/apc-suspends-kebbi-lawmaker/amp/?__twitter_impression=true
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng