Ganduje ya ba matasa 60 tallafin naira miliyan 30 domin gudanar da sana’a

Ganduje ya ba matasa 60 tallafin naira miliyan 30 domin gudanar da sana’a

Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ba wa matasa sama da sittin tallafin naira miliyan 30 bayan sun kammala koyon aikin gyaran babbar mota.

Haka kuma, gwamnan ya ba su kayayyakin aiki na miliyoyin kudi. Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta maida hankali sosai wajen fito da shirye-shiryen samawa matasa sana’a.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Mutum biyu sun mutu, an nemi da dama an rasa sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Yongogba

Mutum 34 daga cikin matsan dai an koya masu gyaran mota ne, 5 masu aikin ruwaya, 16 kuma gyaran na’urar sanyaya wuri wato AC sai kuma mutum 5 kacal daga cikinsu masu yin waldar gas.

Da yake jawabin a wurin bikin yaye daliban da aka koyawa sana’o’in, Ganduje ya ce: “A cigaba da wannan shiri na musamman zamu sake horar da wasu matasa 140 nan bada jimawa ba. Sabbin matasa da za a dauka za a koyar da su yadda aikin kanikancin manyan motoci a cikin watanni uku.”

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnatinsa ta riga da ta horar da matasa 2,690 a kan yadda ake gyaran babur, 560 kuma yadda ake faci ta hanyar amfani da cigaban zamanai, 72 kuma an koya masu gyaran motocin Peugeot ta hanyar amfani da cigaba irin zamani.

Jaridar The Nation ta ruwaito mana cewa, Ganduje ya bayyanawa wakilinta cewa tsarin mai taken ‘Matasa Madogara’ an bude shi ne a yankunan jihar gudu uku, inda gundumar Kano ta tsakiya ke da cibiyoyin horon guda hudu, Kano ta Arewa na da guda uku sai kuma Kano ta Kudu inda take da cibiyoyin uku.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel