Yan Boko Haram sun kashe mutane 3 a Borno, sun kwashe abinci da tumaki

Yan Boko Haram sun kashe mutane 3 a Borno, sun kwashe abinci da tumaki

Akalla mutane uku ne suka rasa ransu yayin da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai wani samame garin Nganzai dake cikin jahar Borno a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba, inji rahoton jaridar Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani shaidan gani da ido, kuma dan banga a yankin daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 9 na dare, inda suka afka kauyen Mallam Kaleri dake kusa da Gajiganna a garin Nganzai.

KU KARANTA:

Baya ga mutane uku da yan ta’addan suka kashe, dan bangan yace sun ji ma wasu mata biyu rauni sa’ilin da suka bude ma mazauna garin wuta a daidai lokacin da suka afka cikin kauyen.

“Yan ta’addan sun kawo hari kauyenmu Malam Kaleri a daren Litinin, kusa da kauyen Gajiganna, sun kashe mutane 3, wadanda tuni mun yi musu jana’iza, sa’annan sun jikkata mata biyu, kuma sun tafi da kayan abinci da tumaki.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari ya sanar da sakin wasu gagga gaggan yan bindiga guda 6 dake kame a hannun gwamnati a sakamakon tattaunawar sulhu da gwamnatin Katsina ta fara yi da yan bindigan.

Masari ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan kafin a kammala tsare tsaren sakin yan bindigan, sai dai gwamnan bai bayyana sunayen yan bindigan ba, saboda tsaro.

A madadin yan bindiga 6 da gwamnan ya saki, ya bayyana cewa yan bindiga zasu sako mutane 20 daga cikin mutanen dake hannunsu a ranar Talata, 10 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel