Wata mata ta maka mijinta kara kotu saboda rashin bata hakkinta na kwanciya da bai yi

Wata mata ta maka mijinta kara kotu saboda rashin bata hakkinta na kwanciya da bai yi

Wata mata mai suna Talatu a ranar Litinin ta kai karar mijinta Nasiru Sulaiman zuwa gaban kotun Shari’a wanda ke zaune a Magajin Gari, Kaduna a dalilin rashin bata hakkinta na kwanciya har tsawon shekaru biyar.

Talatu mai shekaru 35 a duniya wadda ke zaune a shiyyar Makera Kaduna ta shaidawa kotun cewa mijinta ya kwashi tsawon shekara biyar ba tare da ya kusanceta ba.

KU KARANTA:Buhari ya bada umarnin kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu

“Muna da yara shida tare da shi amma ya ki sanya su a makaranta. Na sa su makarantar amma sai ya ciresu yana cewa wai zan sauya masu ra’ayi daga irin fahimtarsa.

“Yau wata tara kenan yaran ba su zuwa makaranta. Gidan da muke zama a ciki baida kyakkyawan yanayi ga beraye ta ko ina, naira 300 kacal yake bani in ciyar da diyanshi bakwai.

“Wani lokacin na kan fita wurin yin aikatau domin sama mana abinda zamu rufawa kanmu asiri, duk da haka kuma sai rika zargina da karuwanci. Na gaji gaskiya saki nake nema yanzu.” Inji matar.

Nasiru Sulaiman wanda shi ne matar mai suna Talatu ke kara a matsayinsa na mijinta ya karyata abinda ta fadi.

“Na taba yin wata tafiya na bar matata da ciki, ko da na dawo sai ta ce min wai ta yi barin cikin, amma ni nasan karya take kawai dai bata so ne ta haihu da ni.” A cewar mijin.

Sulaiman ya amsa cewa yana bata naira 300 kudin cefane saboda ya tanadi dukkanin kayan abinci ya ajiye a gidansa. Bayan sauraron ta bakin mata da mijin, alkalin kotun Murtala Nasir ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Satumba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel