Gwamnan jihar Zamfara ya amince da dawo da malaman makaranta 556 da gwamnatin Yari ta kora

Gwamnan jihar Zamfara ya amince da dawo da malaman makaranta 556 da gwamnatin Yari ta kora

- Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya amince da dawowar malaman makaranta 556 kan aikinsu

- Gwamnan ya umarci shugaban ma'aikatan jihar da ya fara biyan ma'aikatan a watan Satumba

- Gwamnan ya tabbatarwa da ma'aikatan cewa dawo dasu aiki na daya daga cikin burin gwamnatinsa

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da maido da malaman makaranta 556 da gwamnatin da ta gabata ta kora.

Hakan na kunshe ne a cikin takardar da babban daraktan yada labarai na jihar, Yusuf Idris ya sa hannu kuma ya mika ga manema labarai a Gusau ranar Juma'a.

Ya ce tuni gwamnan ya umarci shugaban ma'aikatan jihar da a fara biyan albashin ma'aikatan a watan Satumba.

KU KARANTA: Shahararriyar mawakiyar gwambara, Nicki Minaj ta sanar da daina waka

Matawalle, ya jinjinawa malaman akan hakurinsu da juriya akan lamarin kuma ya horesu da su kasance masu dabi'a ta gari yayin da suka dawo aikin gwamnatin jihar.

Ya ce dawo da su aiki na daya daga cikin burikan gwamnatinsa na sauraro da kuma share kukan masu koke.

A cikin satin ne malaman makarantar 556 suka kai kokensu ga gwamnan inda a take ya umarci shugaban ma'aikatan jihar, Kabiru Balarabe da ya tantance ingancin koken tare da nagartaccen rahoto akan haka.

Bayan binciken shugaban ma'aikatan ya nuna cewa akwai inganci a maganganunsu, sai gwamnan ya amince da dawo dasu bakin aikinsu.

Idan zamu tuna, gwamnan ya dawo da ma'aikata 1,040 cikin 1,400 da gwamnatin Yari ta dauka aiki amma aka ki biyansu albashi har na watanni 18.

Ma'aikatan da abin ya shafa sun bukaci hakkinsu ta hanyar maka gwamnatin a kotu inda suka yi nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel