Ikon Allah sai kallo: Mata mai shekara 73 ta haifi tagwaye bayan shekaru 57 da aurenta (Hoto)

Ikon Allah sai kallo: Mata mai shekara 73 ta haifi tagwaye bayan shekaru 57 da aurenta (Hoto)

Wata mata mai shekaru 73 a garin Andhra Pradesh dake kudancin kasar Indiya ta haifi tagwaye dukkaninsu mata bayan likitoci sunyi mata aiki na musamman a ranar Alhamis.

“Mahaifiyar da tagwayen na cikin koshin lafiya”, kamar yadda Dakta Uma Sankar wanda shi ne likitan matar ya shaidawa BBC Telugu.

Ikon Allah sai kallo: Mata mai shekara 73 ta haifi tagwaye bayan shekaru 57 da aurenta (Hoto)
Ikon Allah sai kallo: Mata mai shekara 73 ta haifi tagwaye bayan shekaru 57 da aurenta (Hoto)
Asali: Twitter

KU KARANTA:Robert Mugabe: Maganganu 10 masu tasiri da yayi a lokacin rayuwarsa

Mangayamma Yaramati tare da mijinta wanda ke da shekaru 82 a duniya ta ce sun dade suna neman haihuwa amma Allah bai ba su ba.

“Muna matukar farin ciki da samun wannan karuwar,” inji Sitarama Rajarao wanda shi ne mahaifin ‘yan tagwayen.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, Mista Rajarao ya samu rashin lafiyar da ta buge inda har aka kwantar da shi a asibiti bayan kwana guda da saukar mai dakinsa.

Da yake amsa tambayar ‘yan jarida game da shekarunsu da kuma yadda rayuwar diyan za ta kasance bisa la’akari da cewa shekarunsu sun ja, Rajarao ya ce: “Babu abinda ke hannunmu dangane da rayuwar wadannan yara, duk abinda Allah ya so ya faru shi ne zai faru, don haka mun mika lamarinmu zuwa ga Allah.”

Samun wannan karuwa ya matukar farantawa ma’aurantan rai, kasancewar sun sha tsangwama daga wurin mutanen kauyensu.

“An sha kirana da suna juya, saboda an ga ban haihu ba. Mun yita ganin likitoci domin neman ko akwai wani taimako da zasu iya mana amma abin ya gagara.” Inji Yaramati.

Matar ta kara da cewa: “Wannan shi ne lokaci mafi farin ciki a rayuwata.”

https://thenationonlineng.net/73-yr-old-woman-gives-birth-to-twins-57-years-after-marriage/amp/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel