An yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin kashe budurwarsa

An yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kama shi da laifin kashe budurwarsa

- An yankewa wani saurayi hukuncin kisa ta hanyar rataya a jihar Ondo

- Kotu ta kama saurayin da laifin kashe budurwarsa ta hanyar daba mata wuka a kirji

- Lamarin ya samo asali ne a lokacin da wata karamar cacar baki ta faru a tsakaninsa, inda shi kuma yayi amfani da wuka ya caka mata a kahon zuci

Wata babbar kotu dake Akure babban birnin jihar Ondo ta yankewa wani saurayi mai suna Saliu Oladayo, mai shekaru 26 hukuncin kisa a ranar Talatar nan da ta gabata 3 ga watan Satumba, bayan kama shi da laifin kashe budurwarsa 'yar shekara 19 mai suna Confidence Ebere.

Jami'an 'yan sanda ne suka kama mai laifin bayan ya dabawa budurwar ta shi wuka a lokacin da suke cacar baki a watan Mayun shekarar 2018, a unguwar Oshinle dake Akure.

KU KARANTA: Tashin hankali: Abinda zai faru da ace lokacin Abacha ne ake kashe mutane a kasar Afrika ta Kudu - Skiibii

Bayan gabatar da kwakkwaran bincike an gano cewa Saliu Oladayo wanda bai jima da kammala makarantar sakandare ba, shi ya dabawa marigayiyar wuka a kirji, a lokacin da suke wata 'yar cacar baki a gida mai lamba biyu dake Dele Ojo cikin garin Akure da misalin karfe 2 na rana.

Da yake yanke hukunci akan wannan lamari, bayan gurfanar da Oladayo a gaban kotun da ake tuhumarsa da kisan kai, mai shari'a Ademola Bola ya yankewa saurayin hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan duka shaidu sun bayyana cewa shine ya aikata wannan laifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel