‘Yan sanda sun kama mutum 21 da ake zargi da aikata fashi da makami a Gombe

‘Yan sanda sun kama mutum 21 da ake zargi da aikata fashi da makami a Gombe

A jiya Talata 3 ga watan Satumba ne rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta samu nasarar damke mutum 21 wadanda suka jima suna addabar garin Gombe da laifukan fashi da makami.

Da take jawabi ga manema a labarai a kan al’amarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Obed Mary Malum ta ce an kama mutanen ne bayan an gudanar da bincike mai zurfi.

KU KARANTA:Kafin karshen shekarar nan zamu gama da kasafin kudin 2020 – Majalisar Dokoki

Ta kara da cewa akwai ‘yan danfara daga cikin mutanen da aka kaman. Gabriel Micahel Alli, dan shekara 18 a duniya an kama shi ne da laifin damfara da kuma cuta ta hanyar amfani da yanar gizo a ranar 30 ga watan Agusta.

Wata mata mai suna Deborah Tanko ce wannan matashin saurayin ya damfara inda yayi amfani da na’ura mai kwakwalwa domin sace mata N187,100 daga asusun ajiyarta na banki.

SP Malum ta kara da cewa an samu miyagun makamai a wurin matashin wadanda suka hada da, wayar salula, N10,000, takalmi kafa biyu da kuma sutura ta kudi N33,000 wanda suke na sata ne.

Bugu da kari rundunar ‘yan sanda ta kara da cewa a ranar 21 ga watan Agusta ta kama wani gun-gun ‘yan fashi jihar ta Gombe.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa dukkanin matasan sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi aikata fashi da makami. Har ila yau an same su dauke da bindigogi, wayoyin salula iri-iri har kala 22, wukake, na’urar laptop da kuma kakin sojoji.

A karshe ta yi kira ga mazauna garin Gombe da su kai rahoton irin wadannan mutanen zuwa ga hukumar ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace a game da su.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel