Emmanuel Nwude: Dan damfarar da ba a taba yin kamar shi ba a Najeriya, ya damfari wani mutumi ta hanyar sayar mishi da filin jirgin sama dungurungum

Emmanuel Nwude: Dan damfarar da ba a taba yin kamar shi ba a Najeriya, ya damfari wani mutumi ta hanyar sayar mishi da filin jirgin sama dungurungum

- Emmanuel Nwude shine dan damfarar da ba a taba yin irinshi ba a tarihin Najeriya dama duniya baki daya

- Domin kuwa ya sayarwa da wani mutumi filin jirgin sama dungurungum wanda kuma babu filin jirgin saman kwata-kwata a duniya

- Lamarin ya faru a tsakanin shekarar 1995 zuwa 1998, inda kuma aka kama shi a shekarar 2004, an kuma sake shi a shekarar 2006

Filin jirgin sama ba karamin waje ba ne idan mutum yayi tunani da kyau, ko iya wajen da jirgi yake gudu ya kafin ya tashi sama ya isa mutum ya kure iya ganin shi.

Abin mamakin a nan shine, yadda aka yi Emmanuel Nwude ya iya sayar da filin jirgin dungurungum wanda kuma babu shi kwata-kwata a duniya.

Sannan kudin da ya sayar da filin jirgin ba wai karamin kudi bane da mutum zai yi tunani, kudin ya kai kimanin dala miliyan dari biyu da arba'in da biyu ($242m), kimanin naira biliyan tamanin da takwas (N88b) a kudin Najeriya.

Lamarin ya faru ne tsakanin shekarar 1995 zuwa 1998 kuma wanda aka damfara wani mutumi ne dan kasar Brazil mai suna Nelson Sakaguchi, wanda a lokacin yake a matsayin darakta na banki.

A lokacin shima Nwude yana kan babban mukami, domin kuwa yana matsayin darakta ne na Union Bank, wannan dalili ne yasa ya samu wannan damar.

Ya sanar da Mr Sakaguchi cewa Najeriya tana shirin gina filin jirgin sama a Abuja, sannan ya sanar da shi cewa akwai yiwuwar ya iya samun sama da dala miliyan goma idan aka kammala aikin.

Wannan daliline yasa Mr Sakaguchi ya biya dala miliyan dari da casa'in da daya ($191m).

KU KARANTA: Innalillahi: Yadda Malam Musa ya kama amaryarsa Fatima tana zina da dan cikinsa akan gadonsu na Sunnah

A shekarar 2004 an fara bincike akan wannan damfara da Nwude yayi, inda a lokacin aka kama da yawa daga cikin yaransa aka gurfanar dasu a gaban wata babbar kotu a Abuja.

Duka masu laifin sun amsa laifinsu, inda kuma aka yi musu gargadin kada su bai wa alkalai masu yi musu shari'a cin hanci.

Kamar kuwa sun sani, domin kuwa a lokacin sai da Nwude yayi kokarin bai wa Nuhu Ribadu cin hanci, wanda a lokacin yake a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, inda yayi masa alkawarin ba shi dala dubu saba'in da biyar ($75,000) amma yaki karba.

A karshe dai Nwude ya amsa laifinsa, inda aka yanke masa hukuncin shekara biyar kuma aka bukaci ya biya dala miliyan goma ($10m).

An sake shi a shekarar 2006 sannan bayan fitowarshi ya bukaci a bashi dukiyarsa, a karshe ya tashi da sama da dala miliyan dari da sittin da bakwai ($167).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel