Fa’idar ajiye zuma a gida, cututtuka 5 da take magani

Fa’idar ajiye zuma a gida, cututtuka 5 da take magani

Zuma dai wata abace wadda banda tsantsar zakin da Allah ya zuba mata na dandano a baki tana da amfani a fanni lafiyar jiki, inda take maganin wadansudangin cututtuka a jikin dan adam.

Idan har baka taba lura da fa’idar zuma ba akwai bukatar ka tanadi kwalba guda ta zuma domin jarabawa. Ga jerin wasu cututtuka guda biyar da zumar ke magani:

1. Zuma na rage yawan yin tari

Zuma na da matukar amfani musamman a lokacin sanyi inda take maganin tari. A cewar kungiyar likitocin yara kanana ta duniya bisa la’akari da wani bincike da ta gudanar zuma ta kasance magani tari ga yara sama da 100. Haka kuma iyayen yara sun tabbatar da wannan zance inda suka ce zuma ta dara sauran magungunan da ake amfani da su domin maganin tarin.

KU KARANTA:Hanyar Kaduna-Abuja: Abokina ya rabu da zuwa gonar kajinsa saboda masu garkuwa da mutane, inji Shehu Sani

2. Zuma na warkar da rauni

Wannan magana nasan za ta ba wasu daga cikinmu mamaki kwarai da gaske. Tun shekaru aru-aru da suka wuce a kasar Masar mutane sun kasance suna shafa zuma a saman rauni idan suka ji ciwo. Har ila yau ana amfani da wannan hanyar domin warkar da rauni a jiki.

3. Zuma tana kara kaifin basira

Yana da matukar muhimmanci mu lura da abinci da muke ci ya zamana wanda zai kara mana kaifin basira ne. Zuma tana karawa mutum kaifin basira da lafiyar kwakwalwar tasa ita kanta tare da ba shi lafiyar jiki kamar yadda masana suka ce.

4. Zuma na taimakawa wurin narkewar abinci a ciki

Zuma nada matukar muhimmacin wurin magance matsalar gudawa inda take taimakawa narkewar abinci a cikin dan adam. Wannan yana rage matsalar gudawa kasancewar abincin zai narke yadda ake bukata a ciki.

5. Zuma na maganin kurajen fuska (finfus)

Zuma idan aka hada ta da sauran nau’in itace irinsu lemun tsami,gayen fiya da sauran wadansu ganyayyakin domin shafawa a fuska su na maganin kurajen fuska wanda aka fi sani da finfus. Mutane da dama wadanda suka yi amfani da wannan maganin sun bamu tabbacin ingancinsa wurin magance kurajen fuskan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel